Fadar Shugaban Kasa tayi bayanin makomar Shugaban INEC da ake rade-radin tsigewa

Fadar Shugaban Kasa tayi bayanin makomar Shugaban INEC da ake rade-radin tsigewa

  • Mai magana da yawun bakin Shugaban kasa ya yi magana a kan rade-radin canza shugaban hukumar INEC
  • Mr. Femi Adesina ya tabbatar da ba za a tsige Farfesa Mahmood Yakubu kamar yadda wasu suke yadawa ba
  • Adesina ya kuma nuna na’urorin BVAS za suyi aiki a zaben 2023, yace shugaban kasa na goyon bayan hakan

Abuja - Femi Adesina wanda yake magana da yawun Mai girma Muhammadu Buhari yace babu abin da zai hana ayi amfani da na’urorin BVAS a 2023.

Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba 2022, inda aka ji Femi Adesina ya yi karin haske game da shirye-shiryen zabe.

Yayin da ake rade-radin cire shugaban INEC, Adesina ya tabbatar da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana goyon bayan Mahmood Yakubu.

Kara karanta wannan

Ba Zamu Yarda Wani Dan Arewa Ya Gaji Buhari Ba: Kungiyoyin Kasar Yarbawa

Da yake bayani a wajen wani taro da aka shirya a kan harkar zabe a Abuja, Hadimin shugaban kasar yace babu dalilin tsige shugaban hukumar zaben.

'Yan jarida na fuskantar barazana

An gudanar da wannan taro na musamman a ranar yakar ta’adin da ake yi wa ‘yan jarida, sai aka yi amfani da damar domin tunkarar magudin zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin CPJ da ke kare hakkin ‘yan jarida yace abokan aikinsu 16 aka hallaka a 2022 a Duniya. Alkaluman UNESCO sun ce an kashe 1200 daga 2006.

Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @femi.adesina.1023
Asali: Facebook

Labaran bogi sun fara yawo

Adesina wanda ‘dan jarida ne da ya zama mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, ya bayyana irin kokarin da suke yi domin kare abokan aikinsu.

Amma Hadimin shugaban kasar ya koka a kan yadda ake yada labaran bogi iri-iri, musamman ganin lokacin zabe ya karaso, ya nuna hakan yana da hadari.

Kara karanta wannan

PDP Za ta Ci Duka Zaben da Za Ayi, Ban da na Kujerar Shugaban kasa Inji Gwamnanta

Daga cikin labaran karya da ake ji a gari shi ne wasu kusoshin jam’iyyar APC mai mulki suna so ayi watsi da BVAS, sannan a kawo sabon shugaban INEC.

Vanguard ta rahoto Adesina yana cewa Shugaban kasa ya yi bayani sau bila-adadin a kan yadda na’urorin zamani suka yi amfani wajen darewarsa kan mulki.

Hadimin yace yadda aka shigo da PVC domin a rage murdiya a zabe, haka aka fito da na’urorin BVAS, kuma babu abin da zai sa a ki amfani da su a zaben badi.

Kwankwaso ya fito da manufofi

Daga batun hadin kai da kawo zaman lafiya zuwa bin doka da tsarin mulki, kun ji labari Rabiu Kwankwaso ya kaddamar da manufofin takara mai shafuka 160

Gwamnatin Rabiu Kwankwaso da NNPP tace za ta farfado da tattalin arziki, ta samar da ayyuka, a maida ganin likita kyauta, kuma a dawo da kimar Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu: Abin da Buhari Ya Fada Mani Yayin da Na Nemi Ya Zakulo Mani Mataimakina

Asali: Legit.ng

Online view pixel