‘Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun yi wa Basarake Yankan Rago a Najeriya

‘Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun yi wa Basarake Yankan Rago a Najeriya

  • Wasu ‘yan bindiga da ake tunanin adadinsu ya haura 70 sun kai hari a wani kauye Tunga Rafi a jihar Kebbi
  • ‘Yan bindigan sun kashe Hakimin garin, Abubakar Magaji (Sabo Rafi), kuma sun yi awon gaba da iyalinsa
  • Mutane hudu suka mutu a harin da aka kai, amma an bar mutane da-dama su na jinya a sakamakon rauni

Kebbi - ‘Yan bindiga sun kai hari a kauyan Tunga Rafi a karamar hukumar Augie a jihar Kebbi. The Guardian ta fitar da wannan rahoto a makon nan.

A sanadiyyar wannan hari da aka kai, an hallaka mutane akalla hudu a Tunga Rafi. Baya ga haka, ‘yan bindigan sun bar Bayin Allah da-dama da rauni.

Wani mazaunin wannan kauye ya shaidawa manema labarai adadin ‘yan bindigan da suka auko Tunga Rafi a daren na ranar Alhamis, sun haura 70.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun dura kan manoma, suna shirin kakaba musu haraji

Mai garin kauyen wanda aka bada sunansa a matsayin Abubakar Magaji, yana cikin wadanda aka kashe. Jaridar Aminiya tace ‘yan bindigan sun yanka shi.

An kashe Hakimi, an dauke iyalinsa

Bayan yi wa Basaraken yankan rago, wani ‘dan banga da ya yi magana da ‘yan jarida a boye, yace ‘yan bindigan sun yi awon gaba da mai dakin Sabo Rafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoton da aka fitar, an ji har da yaron Hakimin aka dauka, ana zargin an yi garkuwa da su. Jami’an ‘yan sanda sun ce ba su da aukuwar abin ba.

Sojoji
Sojoji a Kebbi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Harin farko a Tunga Rafi

A cewar ‘dan bangan, yayin da suka fara shiri domin su aukawa miyagun, sai suka tsere, yace wannan ne karo na farko da aka kawowa garin na su hari.

“Sun tsere daga kauyen lokacin da suka fahimci mutanenmu sun fara taruwa domin su auka masu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace dan takarar majalisa na jihar Zamfara

"Wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suke kawo hari a kauyen nan, duk da miyagun sun addabi makwabtanmu a lokutan baya-bayan nan."
“Mutanenmu sun fito da yawa a kauyen domin su maida masu martani, amma sun hallaka Mai garinmu da wasu mutane uku, sai suka arce."

- 'Dan banga

Yayin da suke ficewa daga kauyen, ‘yan bindigan sun kashe wasu mutane biyu a kan hanyarsu.

An kashe 'yan bindiga a Zamfara

Rahoto ya zo cewa wani 'dan kato da gora da yake rike da bindiga a lokacin da aka kawo hari a kasuwar Zamara, ya yi kukan kura, ya kashe wasu miyagu.

Amma da yake Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi, ‘yan bindigan sun fatattaki mutane daga kasuwar Gidan Goga a jihar Zamfara, suka ci karensu babu babbaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel