Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Kera Mota “Bugatti” Daga Tarkacen Shara, Ya Tuka Kayarsa

Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Kera Mota “Bugatti” Daga Tarkacen Shara, Ya Tuka Kayarsa

  • Wani matashi mai suna @mrtech170 a kafar TikTok ya nuna kalar mota 'Bugatti' da ya kera daga tarkacen shara
  • A bidiyon da ya yada a shafinsa, matashin ya nunawa mutane yadda ya faro aikin da kuma irin kokarin da ya yi
  • Mutane da dama sun yi mamaki, sun bayyana martaninsu da ganin wannan mota da ya kera mai ban mamaki

Wani hazikin matashi mai suna @mrtech170 a kafar TikTok ya nuna bidiyon yadda yake shakatawa da wata wakar Rick Ross mai taken 'Stay Schemin' yayin da yake tuka wata motar da ya kera

A gaban motarsa an rubuta lamba '16', wanda ake ganin kamar an yi sa da kwali ne.

A wasu tsoffin faya-fayan bidiyon dake kan shafinsa, an ga lokuta da dama na yadda matashin ke aikin kera motar. An ga yadda ya saka taya da fangami da dai sauran sassan jikin motar.

Kara karanta wannan

Amarya Ta Fada Tashin Hankali Yayin da Aka Bindige Angonta Ranar Aurensu

Matashi ya kera Bugatti, ya tuka kayarsa
Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Kera Mota “Bugatti” Daga Tarkacen Shara, Ya Tuka Kayarsa | Hoto: TikTok/@mrtech170
Asali: UGC

Matukin motar dai an ga kamar takardar nade abinci aka yi amfani da ita wajen yinsa. Ga kuma haske da dai sauran kaya masu kyau a jikin motar, kwanin ban sha'awa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akwai akalla mutane 700 da suka yi martani tare da dangwale kusan 70,000.

Legit.ng ta tattaro kadan daga abin da mutane ke cewa kamar haka:

Alungile Alue yace:

"Ina masu son ganin wannan motar tana motsi?"

terminator56402 yace:

"Ana ta yada jita-jitan cewa wai ta baya ake tura motar."

nokuzolananantenh yace:

"A da yadda na yi tsammani, motar nan ba za ta yi motsi ba."

Nikkimapakisha yace:

"Kai, kana wuta sosai kuma nima daga Bergville Bhethany nake amma a Durban nake rayuwa, ina matukar alfahari da kai.

Noluthando Shelembe yace:

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za su iya faruwa idan CBN ya buga sababbin N200, N500 da N1000

"Kai, wasu dai akwai fikira. Wannan shine tsagwaron basira."

SPRINKLERSSSS yace:

"Allah ya kareka daga dukkan wani hasken dake fitowa daga cikin gida. Amin."

Bloom yace:

"Mutanen kirki kadai kake bukata su gani daga nan ka tafi."

Bayan Mutuwar Sarkin Kazaman Duniya, an Gano Magajinsa Daga India

A wanu labarin, bayan tabbatar da mutuwar mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, Amou Haji, an samu wani dan kasar Indiya da ake tunanin shi ne zai zama magajinsa a wannan dabi'a ta kazanta.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, ana kyautata zaton Kailash 'Kalau' Singh ne zai maye gurbin Haji, wanda shi ma aka ce ya shafe shekaru da dama bai taba ruwa ba.

A shekarar 2009, jaridar Hindustan Times ta ruwaito cewa, Kailash, wanda ya taso daga wani kauye dake wajen birnin Varanas, ya shafe shekaru 35 bai yi wanka ba, kusan shekaru 49 kenan zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure

Asali: Legit.ng

Online view pixel