Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63

Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63

  • Dattijuwar mata ‘yar asalin jihar Legas mai shekaru 63 mai suna Amdalat Taiwo Pedro ta bada labarin dalilin da yasa ta fada sana’ar kwashe bola
  • Matar mai shekaru 63 a duniya ta rasa mijinuts tun shekaru 10 da suka gabata kuma ‘dansu daya ya rasu ya bar mata jikoki biyu
  • Sirikar Amdalat ta arce zuwa gidan iyayenta kuma kasuwancin da take yi ba zai rike su ba bare a samu kudin makaranta da na haya

Legas - Amdalat Taiwo Pedro mata ce da mijinta ya mutu amma take sana’ar kwashe bola a titinan Legas a kokarinta na samun abinda zata ci da kuma kula da kanta.

Amdalat Taiwo
Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63. Hoto daga @bbcnewspidgin
Asali: Twitter

Sakamakon hauhawar farashi da tsananta rayuwa a kasar, mutane da yawa sun kama sana’o’i wadanda a baya ba zasu taba yin su ba, BBC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Yaushe matar ta fara kwashe bola?

Pedro wacce ta kasance matar da ta rasa mijjnta tun shekaru goma da suka gabata ta bayyana cewa ta fara kwashe bola sama da shekaru bakwai da suka gabata kuma har yanzu sana’ar take yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mutane da yawa da suka zage ni kan na fara kwashe bola sun bi ayari sun fara yi kamar ni.”

- Ta tuna abinda suka fuskanta.

Wadanne kalubale matar ke fuskanta?

Kamar yadda tace, kudaden da take samu ba su iya isarta da iyalanta, hakan yasa ta koma tsintar robobin inda ta kara da cewa ‘yan jari bola inda ta kara da cewa ana biyansu duba da yawan robobin da suka kawo.

Bayan mutuwar mijinta da shekaru 10, ‘dan Amdalat ya rasu inda ya bar ta da jikoki biyu. Sirikarta ta koma gidan iyayenta.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Bayyana Yadda Kidinafas Suka Bata N2,000 Bayan Karbar N6m daga Mijinta

“Ina amfani da kudin wurin kula da jikokina saboda babu mai taimaka min.”

- Tace.

Kudaden da nake samu ina zuba su ne kan ilimin jikokina

Tsohuwar mai shekaru 63 ta bayyana cewa kudin da take samu daga kwashe bolar tana amfani dasu ne wirin ciyar da jikokinta, biyan kudin makaranta da haya.

“Mafi karancin kudin da nake samu shine N20,000 kuma mafi yawan kudin da nake samu shine N120,000. Ina tashi karfe 5 na safe in yi ayyukan gida zuwa karfe 7 sannan ina bar gidan tare da shiga titi fara kwashe bola.”

Ta kara da cewa jikokinta suna taimaka mata wurin kwashe bolar tare da kai su inda za a siya.

Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo

A wani labari na daban, matar aure kuma mahaifiyar yara biyu wacce direban tasi ce wacce ta shawarci sauran mata da kada su saki jiki ba tare da neman na kansu ba.

Kemi Toriola wacce mahaifiyar yara biyu ce ta shiga sana’ar tukin tasi bayan annobar COVID-19 ya yi matukar illa ga kasuwancinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel