Najeriya Na Zaman Tsammani Yayinda China Taci Kenya Tara Kan Rashin Biyan Bashi Kan Lokaci

Najeriya Na Zaman Tsammani Yayinda China Taci Kenya Tara Kan Rashin Biyan Bashi Kan Lokaci

  • Yayinda kasashen Afrika suka kwashe shekara da shekaru suna karban basussuka, kasar Sin ta fara daukan mataki
  • Kamar dai Najeriya, kasar Kenya ta ci basussukan biliyoyi daga wajen kasar China kuma ta gaza biya
  • Gwamnatin kasar Sin ta ci Kenya taran N4.71 billion saboda jinkiri wajen biyan kudin bashin da ake binta

Gwamnatin kasar Sin ta bukaci kasar Kenya ta biyar tarar Sh1.312 billion(N4.71 billion) bisa jinkiri wajen biyan kudin bashin da ake binta.

Sin ta baiwa Kenya bashin kudaden ne don gina layin dogon jirgin kasa amma sun gaza samun isasshen kudin shiga don biyan bashin.

Jaridar BusinessDaily Kenya ta ruwaito cewa kasar ta karbi bashin rabin Tiriliyan na Shillings daga wajen Kasar China, don gina layin dogon Mombasa zuwa Naivasha.

Kenya
Najeriya Na Zaman Tsammani Yayinda China Taci Kenya Tara Kan Rashin Biyan Bashi Kan Lokaci Credit: Etienne Oliveau
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin shigan da aka samu na cinikin layin dogon ya gaza yadda ake tsammani, Nation Africa ta ruwaito.

A cewar rahoton:

"Wannan taran na (Sh1.312 billion) kudin ruwa ne wanda yayi daidai da 1% na asalin bashin."
"(Kamfanin layin dogon) SGR ya biya Sh22 billion cikin kudin bashin kawo watan Yuni amma ya fadi Sh3.4 billion."

Darasi ga Najeriya

Kawo karshen Yunin 2022, ofishin manejin basussuka ya bayyana cewa kasar Sin na bin Najeriya bashin $3.92bn.

Hakazalika a kasafin kudin 2023 da shugaba Buhari ya gabatar makon da ya gabata, za'a sake cin wani sabon bashin N10.78 trillion.

Tuni dai gwamnatin Sin ta daina baiwa Najeriya bashi saboda wasu dalilai.

Jinkirin Ginin Layin Dogon Kaduna Zuwa Kano: China Ta Hana Najeriya Bashi

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ya ce gwamnatin Najeriya na jiran ƙarin rancen kuɗaɗe ne daga ƙasar Sin domin ƙarasa ayyukanta na layin dogo.

Ayyukan layin dogon dai sun haɗa da: layin dogo na Abuja zuwa Kano da Fatakwal zuwa Maiduguri.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja, a ranar Juma’ar nan, cewa rashin ƙarasa aikin laukan dogon ya faru sakamakon rashin samun kaso 85 cikin ɗari na rancen da ta nema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel