Gwarzon Malamin Shekara A Jihar Legas Ya Samu Kyautar Kudi N20,000

Gwarzon Malamin Shekara A Jihar Legas Ya Samu Kyautar Kudi N20,000

  • An raina Malaman Makaranta, Haba Dai Ya fi karfin a bashi wannan dan karamin kudin: Martanin yan Najeriya
  • Dukkan kokarin da nike wajen karantar da dalibai ba don kudi nike yi ba, cewar Malaman Raheem
  • Daukacin Musulman Najeriya sun taya shi murnar zama gwarzon malamin shekara a jihar Legas

Wani Malamin makaranta, Malam Adekoya Raheem, ya zama gwarzon malamin shekarar 2022 na yankin Education District IV dake jihar Legas, Kudu maso yammacin Najeriya.

Raheem dai malami ne a makarantar Sanya Senior Grammar School, Ijeshatedo, Surulere Lagos.

Ya bayyana hoton taron karramashi tare da takardar kudin da kungiyar Action for Change and Empowerment, ta bashi N20,000.

Yan Najeriya da dama sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan tagomashi.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

Adekoya
Gwarzon Malamin Shekara A Jihar Legas Ya Samu Kyautar Kudi N20,000 Hoto: Muslim News
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba don kudi nike karantarwa ba

A hirarsa da jaridar MuslimNews ranar Juma'ar da ta gabata, Raheem ya bayyana cewa bai taba tunanin zai samu karramawa irin wannan ba.

Yace shi dai bai raina kudi N20,000 da aka bashi ba kuma ya gode sosai.

Yace:

"A ranar fa kawai zuwa nayi don an gayyace ni. Ina son bayyana cewa ba don kudi nike abinda nike yi ba, karantarwa abu ne da nike jin dadin yi."
"Ko na samu lada a duniya ko ban samu ba, akwai lada a lahira."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel