Malaman Jami’o’in Gwamnati Sun Rabu 3 a Kan Janye Dogon Yajin-Aikin ASUU

Malaman Jami’o’in Gwamnati Sun Rabu 3 a Kan Janye Dogon Yajin-Aikin ASUU

  • Malaman jami’o’i sun kada kuri’a domin yanke hukunci a kan dogon yajin-aikin da ake yi a Najeriya
  • A wasu rassan na kungiyar ASUU, an zabi a daina yajin-aiki, a wasu jami’o’in akasin hakan ne ya faru
  • Akwai ‘ya ‘yan ASUU da suka bada shawarar a hakura da yajin-aikin, a koma karantarwa a jami'o'i

Abuja - Idan abubuwa ba za su canza ba, a yau Alhamis, 13 ga watan Oktoba 2022, ake sa ran malaman jami’a za su yi taronsu na majalisar ASUU NEC.

Babu mamaki a karshen taron na NEC, a ji kungiyar ASUU ta bada sanarwar cewa ta janye yajin-aiki, hakan za isa daliban jami’io’i su koma makaranta.

Malaman jami’a a karkashin inuwar ASUU suna yajin-aiki tun farkon shekarar nan ta 2022.

Kara karanta wannan

Za a Tarawa Kwankwaso, NNPP Kuri’u Miliyan 5 a Jihar Kano a Zaben Shugaban kasa

Bayan zaman da shugabannin ASUU na kasa suka yi da shugaban majalisar wakilan, sun yanke shawara za su tattauna da junansu kan komawa aiki.

An yi zabe a jami'o'i

A wajen wannan tattaunawa, an yi zabe a rassan kungiyar 123 domin cin ma matsayar ko kungiyar za ta cigaba da yajin-aiki ko za a bude aji.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon kuri’un da ‘Yan ASUU suka kada ya nuna cewa wasu jami’o’i sun gamsu a daina yajin-aikin, wasu kuma sun ce ka da a dawo aiki a haka.

Jami'ar ABU Zaria
Jami'ar ABU Zaria Hoto: @abuzaria_dua
Asali: Twitter

A irinsu jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife, malaman ba su cinma wata matsaya yayin da aka yi taron ASUU a ranar Laraba da nufin tsaida magana ba.

A janye yajin-aiki da sharadi

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ‘Yan ASUU na reshen jami’ar ABU Zaria sun zabi a janye yajin-aikin da sharadin gwamnati za ta biya masu duk bukatunsu.

Kara karanta wannan

Tsohon ‘Dan Wasan Real Madrid Ya Ba Jama'a Mamaki Da Yace Maza Yake Sha’awa

Wani malamin jami’a ya shaida mana ya kamata shugaban kasa ya yi magana kafin zaman na su, ta haka ne za su san abin da za su tattauna a kai a taronsu.

Rahoton yace ba a cin ma matsaya a taron da kungiyar malaman tayi a jami’ar Nnamdi Azikiwe ba.

Za a saba umarnin kotu?

‘Yan ASUU na jami’oin FUTO Akure da na jami’ar Adekunle Ajasin a Ondo sun zabi a daina yaji-aiki, ba don komai sai saboda gudun a sabawa umarnin kotu.

Malaman da ke koyarwa a jami’ar Usman Dan Fodiyo a Sokoto sun zabi a dakatar da dogon yajin-aikin, ta haka ne za ayi biyayya ga hukuncin da aka yi a kotu.

Za mu ba ilmi muhimmanci

Ku na da labari Rabiu Musa Kwankwaso mai neman shugabancin Najeriya a inuwar NNPP ya yi alkawarin bunkasa harkar ilmi idan ya iya kafa gwamnati.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ranar Alhamis Zamuyi Ganawar Gaggawa Don Yanke Shawara Kan Yajin Aiki, ASUU

Kamar yadda ake ganin ya yi a jihar Kano, ‘Dan takaran shugaban kasar na 2023 yace gwamnatinsa za ta tallafawa matasa idan ya yi nasara a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel