Tsohon ‘Dan Wasan Real Madrid Ya Ba Jama'a Mamaki Da Yace Maza Yake Sha’awa

Tsohon ‘Dan Wasan Real Madrid Ya Ba Jama'a Mamaki Da Yace Maza Yake Sha’awa

  • A wasu ‘yan gajerun mintuna a makon jiya, Iker Casillas ya zama wanda yake bin ‘yanuwansa maza
  • Tsohon ‘dan wasan kwallon kafan na Sifen ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa shi manemin maza ne
  • Daga baya an goge wannan magana daga dandalin, Casillas yace bai neman maza, kutse aka yi masa

Spain - A ranar Lahadin da ta wuce ne ake zargin Iker Casillas ya yi magana a shafinsa na Twitter inda ya bada sanarwar cewa maza yake sha’awa.

Jim kadan bayan ya bada sanarwar nan a shafin sada zumuntan, sai aka ji Iker Casillas yana karin haske cewa ba daga gare shi ne maganar ta fito ba.

BBC ta rahoto tsohon ‘dan kwallon yace wasu ne suka kutsa shafinsa, suka ci albasa da bakinsa.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika

Amma kafin Casillas ya goge maganar, wasu a cikin mabiya miliyan 10 da ke bibiyarsa a dandalin Twitter sun gani, har sun fara tofa albarkacin bakinsu.

Me Iker Casillas ya rubuta?

"Ina fatan za ku girmama ra’ayina, Ni maza nake sha’awa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Iker Casillas

Tsohon ‘dan wasan mai tsaron gida ya dawo ya bada hakuri ga wadanda ba su ji dadin maganar ba. Masu neman 'yanuwansa sun fusata da maganar.

Iker Casillas
Iker Casillas Hoto: www.the-sun.com
Asali: UGC

“An yi wa shafina kutse. Amma an yi sa’a, komai ya dawo daidai. Ina ba mabiyana hakuri. Haka zalika al’ummar da ke tare da LGBT.”

- Iker Casillas

Yadda Puyol ya jawo maganar

Legit.ng Hausa ta fahimci an yi wannan gajeren bayani daga shafin Casillas mai shekara 41 ne bayan Carles Puyol ya maida masa martani a dandalin.

Tsohon kyaftin din na kungiyar Barcelona yake cewa ya kamata mu sanar da su game da kanmu. Shi ma daga baya Puyol ya yi maza ya goge maganar.

Kara karanta wannan

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

Rahotanni sun ce tsohon ‘dan bayan ya nemi afuwar mabiyansa, yana cewa ba’a kurum yake yi, tauraron yace bai yi ba'ar da nufin wulakanta kowa ba.

Saura kiris Casillas ya bar tarihi

Skysports tace da Casillas bai goge maganar, ya lashe aman shafin na sa ba, da ya zama tauraron kwallo mafi shahara wanda ya kama wannan layi.

Kasashen Turai da-dama suna ta kokarin yada manufofin LGTBQ+ domin ba mutane ‘yanci su nemi duk wanda suke so tsakanin maza da kuma mata.

Za ayi fim a wajen Duniyar 'Dan Adam

Kun samu rahoto cewa Tom Cruise yana shirin fita daga wannan Duniya da muke rayuwa domin ya shirya wasan kwaikwayo a shekara mai zuwa.

‘Dan wasan zai fito a wani fim da Doug Liman – mutumin da ya shirya wasan The Bourne Identity. Ba a taba jin an bar Duniya saboda shirin fim ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel