A Shekaru 3 a Ofis, Mun Kammala Ayyuka Fiye da 2000 a Ma’ikatarmu – Isa Pantami

A Shekaru 3 a Ofis, Mun Kammala Ayyuka Fiye da 2000 a Ma’ikatarmu – Isa Pantami

  • Ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na zamani tayi ikirarin yin ayyuka sama da 2000 a fadin tarayyar kasar
  • Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami yace duk sun yi wannan kokari ne a cikin shekaru uku da suka yi a ofis
  • Wannan bayani ya fito daga bakin Isa Ali Ibrahim Pantami lokacin da ya ziyarci kamfanin Galaxy Backbone

FCT, Abuja - Ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na zamanin tarayya tace ta kammala ayyuka fiye da 2000 a cikin shekaru ukun nan da suka gabata.

Premium Times ta rahoto Isa Ali Ibrahim Pantami yana cewa haka a lokacin da ya kai ziyara domin ganin aikin kamfanin Galaxy Backbone a garin Abuja.

A wajen ziyarar ne Ministan yace ba makarantu kurum za su amfana da cibiyar bayanan kamfanin GBB ba, har ‘yan kasuwa da sauran jama’a za su amfana.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Kotu Ta Fadawa ASUU da Gwamnati Yadda Za Su Shawo Kan Sabaninsu

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami yake cewa makarantun gwamnati da na ‘yan kasuwa da sauran al’umma za su ci moriyar ayyukan da kamfanin ke yi.

Makarantu za su amfana da karfin sabis yayin da sauran jama’a za su samu horaswa na musamman. Ministan ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na Twitter.

Yadda za a ci moriyar GBB - Minista

“Idan kuka duba wurin nan, cibiyar horaswa ne. Horaswar nan kuma na duka ‘yan Najeriya ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a rika gudanar da horaswa daga lokaci zuwa lokaci domin al’umma saboda a rage adadin marasa kimiyyar zamanin.”

- Isa Ali Pantamu

Pantami
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a GBB Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Mutane za su samu saukin samun aiki

Mai girma Ministan yace idan jama’a suka samu horo da kyau, wannan zai taimaka masu wajen samun aiki a gwamnati ko kamfanoni ko a kasashen waje.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

Pantami yace akwai damammaki barkatai da suke jiran mutane, musamman a kasashen waje. A jawabinsa, Ministan ya bada shawara a nemi aiki a ketare.

Ba da dadewa ba ma’aikatar tarayyar take sa ran kamfanin Galaxy Backbone ya karasa gina cibiyar da yake ginawa a Kano, wanda zai taimakawa yankin.

DG Galaxy Backbone ya yi magana

Darekta Janar na kamfanin, Mohammed Abubakar yace irin wadannan cibiyoyi ne ke bunkasa harkar kimiyyar bayanai da sadarwa na ICT a Duniya.

An rahoto Mista Abubakar yana mai cewa yanzu bayanai sun zama gwal ko danyen mai. Duk wanda yake da bayanan da ake bukata, shi ne mai kudi.

Najeriya ta koma ITU

A makon jiya muka samu labari Najeriya tayi nasarar sake shiga cikin ‘yan kungiyar International Telecommunications Union na Duniya.

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya jagoranci Najeriya ta bada tazarar da ba a taba gani a ITU ba a zabukan da aka shirya a kasar Romaniya.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel