'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Jihar Taraba, Sun Kaahe Rayuka Sama da 10

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Jihar Taraba, Sun Kaahe Rayuka Sama da 10

  • Yan bindiga sun kai wani mummunan hari kan wani ƙauye a ƙaramar hukumar Bali, jihar Taraba ranar Lahadi
  • Arɗo Bello, wani shugaban Fulani a garin da lamarin ya faru yace da farko makasan sun nuna tamkar 'yan Banga ne
  • Yace daga baya kuma suka buɗe wa mutane wuta, kakakin yan sanda yace tuni aka damke waɗanda suka kai harin

Taraba - Wasu tsagerun yan bindiga sun kashe akalla mutum 12 a ƙaramar hukumar Bali, jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya ranar Lahadi.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Mubizen, wata rugar Fulani a yankin masarautar Pangri.

Harin yan ta'adda a Taraba.
'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Jihar Taraba, Sun Kaahe Rayuka Sama da 10 Hoto: premiumtimesng
Asali: Twitter

Wani shugaban Fulani, Arɗo Bello, ya shaida wa sashin Hausa na BBC cewa maharan sun shiga Rugar sanye da Kaki kuma suka nuna tamkar Yan Banga ne kafin daga bisani su ƙaddamar da nufinsu.

Kara karanta wannan

Muhimmin Abun Da Zan Yi Idan Na Ɗare Kujerar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 2023, Kwankwaso

Bello yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yan bindigan sun ce sun shiga yankin ne domin kama wasu da ake zargi, ana haka ne suka buɗe wa mutane wuta ba tare da sun gamu da tirjiya ba, nan take suka kashe mutum 12."

Bello ya ƙara cewa mutane 50, mafi yawansu mata da ƙananan yara, har yanzun babu ɗuriyarsu tun bayan harin. Yace maharan sun yi awon gaba da Shanu 130 daga ƙauyen.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya tabbatar da kai harin ga manema labarai.

Yace tuni suka kama waɗan da ake zargi da hannu a kai harin, wanda ya yi ajalin rayukan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Garin da lamarin ya faru na da nisan kilo mita 30 zuwa garin Bali, hedkwatar ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Wani Gwamnan Arewa Ya Fusata, Ya Dakatar da Biyan Malaman Jami'ar Jiharsa Albashi

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Ɗan Takarar NNPP Wuta a Jihar Arewa

Kwamishinan muhalli da ma'adanai da bai jima da sauka daga muƙaminsa ba a jihar Nasarawa, Musa Ibrahim Abubakar, ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a baya-bayan nan Mista Abubakar ya fice daga jam'iyyar APC bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani na fidda yan takarar majalisar jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel