Yadda ‘Yan Sanda Suka Cafke Barayin da Suka Sace Motar Liman Yana Huduba

Yadda ‘Yan Sanda Suka Cafke Barayin da Suka Sace Motar Liman Yana Huduba

  • A ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba 2022, wasu barayi suka sace motar Sheikh S. S Abubakar
  • Wannan abin takaici ya faru ne a babban masallacin Juma’a na ITN da ke garin Zaria a Kaduna
  • Da yake an taki sa’a, bayan mutane sun baza cigiya a shafin Facebook, sai ga shi an ga motar a Kano

Babban malami Salihu S. Abubakar shi ne ya jagoranci sallar juma’a a ranar bayan ya gabatar da huduba a kan bin kiran Allah da Manzonsa da Kur'ani.

Bayan an idar da sallar aka nemi motar malamin kirar Hilux, aka rasa. A karshe sai dai shehin malamin ya koma gidansa a Zango a wata mota dabam.

Nan take aka bazama sanar da jama’a da hukuma kan abin ya faru. Kuma wannan labari ya karade shafuka da dandalin sada zumunta tun a lokacin.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Zai Karrama Limamin Da Ya Boye Kiristoci A Lokacin Fadan Filato Da Lambar Yabo Mai Girma

Wani malamin jami’a, Dr. Mustapha Auwal Imam yana cikin wadanda suka bada sanarwa a Facebook, wanda wannan ya sa labarin ya shiga wurare.

Daga shafinsa ne gidan rediyon nan na Arewa Radio suka dauki labari, suka wallafa.

Mun kama barayin motar malam - 'Yan Sanda

Bayan kwana biyu da yin wannan, sai ga sanarwa daga Kakakin ‘yan sanda na rundunar reshen jihar Kano cewa an yi nasarar gano wannan mota.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Motar Limamin ITN
Motar Limamin Masallacin ITN Hoto: ITN Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Abdullahi Haruna Kiyawa yace sun yi ram da mutane biyu da ake zargi da laifin satar, ya kuma bada lambar da masu motar za su tuntube shi.

Jaridar Legit.ng Hausa ta tuntubi gidan malamin domin tabbatar da jin gaskiyar lamarin.

A ranar Lahaid, 2 ga watan Oktoba, 2022, daya daga cikin ‘ya ‘yan wannan malami ya shaida mana ta wayar salula cewa lallai an gano wannan mota.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Gano Gawar Wata Mata a Ofishin Shugaban Wani Babban Asibitin Arewa

Yadda Facebook ya taimaka

Da yake bayani a shafin Facebook, Auwal Mustapha Imam, Ph.D yace ya yada labarin ne domin ganin an gano motar, kuma aka yi dace hakan ta faru.

Auwal Imam yake cewa bayan ya bada cigiyar motar a shafinsa, sai labarin ya kai ga gidan rediyo, a sanadiyyar haka wasu suka ga motar a jihar Kano.

Ana haka sai wani da ke bibiyar malamin jami’ar a dandalin sada zumuntar ya ga motar a wajen kanikawa a wani gareji a yankin Ɗorayi/Panshekara.

Nan take shi kuma ya sanar da wani ‘dan jarida, Bashir Sarki Abdulqadir. Ana haka ne sai aka tuntubi jami’an ‘yan sandan Kano domin a ankarar da su.

Da aka yi magana da mai motar a Zaria, sai ya tabbatar da cewa ita ce aka gani a Kano. A karshe dai aka yi ram da wadanda aka samu da motar a gareji.

Kara karanta wannan

Tsaffin Hotunan Gogarman Mai Garkuwa Da Mutane John Lyon Yana Bikin 'Birthday' A Cikin Banki Sun Bayyana

Sheikh Abduljabbar a Kotu

A makon jiya aka ji labari Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara yace ya ba lauyansa kudi har N2m da nufin a shawo kan Alkali, ya fito da shi daga magarkama.

Abduljabar Nasiru Kabara yace an ba Alkali N1.3m, Lauyansa Dalhatu Shehu-Usman ya tashi da N500, 000. Sai dai duk sun karyata wannan zargi mai nauyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel