Shugaba Buhari Zai Karrama Limamin Da Ya Boye Kiristoci A Lokacin Fadan Filato Da Lambar Yabo Mai Girma

Shugaba Buhari Zai Karrama Limamin Da Ya Boye Kiristoci A Lokacin Fadan Filato Da Lambar Yabo Mai Girma

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa sunan malamin nan na Musulunci a jihar Filato, Abdullahi Abubakar, cikin mutane 437 da za a karrama
  • Mallam Abubakar shine limamin masallacin da ya boye kiristoci cikin masallacinsa a lokacin fadan Filato a 2018
  • Hakazalika sunan Muktar Gulma, malamin FGC Birnin Yauri da ya tsaya tare da dalibansa lokacin farmakin yan bindiga ya samu shiga sahun masu karbar lambar yabo ta MON

Abuja - Gwamnatin tarayya ta zabi shahararren malamin nan na Musulunci a jihar Filato, Abdullahi Abubakar, cikin mutum 437 da za ta baiwa lambar girma ta kasa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa gwamnatin ta zabi mallam Abubakar cikin wadanda zasu karbi lambar girma ta MON.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai gabatar da lambar yabon a ranar 11 ga watan Oktoba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Babban Lambar Yabo Na Kasa

Mallam Abdullahi Abubakar
Shugaba Buhari Zai Karrama Limamin Da Ya Boye Kiristoci A Lokacin Fadan Filato Da Lambar Yabo Mai Girma Hoto: The Cable
Asali: UGC

Idan za ku tuna, Abubakar shine limamin da ya boye wasu kiristoci 262 a cikin masallacinsa lokacin da wasu da ake zaton yan bindiga ne suka farmaki garuruwa 10 a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato a watan Yunin 2018.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi kan dalilinsa na aikata hakan, malamin ya bayyana abun da ya aikata a matsayin buga ca-ca da rayuwarsa.

Ya ce:

“Ban taba shiga irin wannan mummunan hali ba a rayuwata. Mummunan abun da ya faru bai taba faruwa ba.”

Wannan abu da ya aikata ya ja masa farin jini a fadin kasar sannan a 2019, kasar Amurka ta karrama malamin da lambar yabo.

Hakazalika an zabi Muktar Gulma, malamin da ya tsaya tsayin daka tare da dalibansa a lokacin farmakin da yan bindiga suka kai kan kwalejin gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri a jihar Kebbi cikin wadanda za a karrama.

Kara karanta wannan

Shahada: Halin Da Na Shiga Sakamakon Karban Addinin Musulunci, Wani Dan Jihar Enugu

Gulma wana aka saka tare da wasu daga cikin dalibansa na cikin wadanda za su amshi lambar yabo ta MON.

Buhari Zai Karrama Sarkin Kano, Sarkin Zazzau Da Wasu Sarakuna 18 Da Lambar Girma Ta Kasa

A baya mun ji cewa an saki jerin sunayen mutanen da gwamnatin Najeriya za ta karrama da lambar girmamawa ta kasa na wannan shekarar.

Legit.ng ta rahoto cewa mutane 437 ne za su samu lambar yabo daga bangarori daban-daban na rayuwa kama daga yan siyasa, yan kasuwa, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da kuma masu nishadantarwa.

Lambar yabon wannan shekarar ya hada da GCON biyar, CFR 54, CON 67, OFR 64, OON 101, MFR 75, MON 56 da FRM 8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel