Tashin Hankali: An Gano Gawar Wata Mata a Ofishin Shugaban Wani Babban Asibitin Arewa

Tashin Hankali: An Gano Gawar Wata Mata a Ofishin Shugaban Wani Babban Asibitin Arewa

  • Jama'ar gari da jami'an tsaro sun kadu matuka bayan an gano gawar wata mata binne a ofishin shugaban babban asibitin Kiama da ke jihar Kwara
  • An dai gayyaci Dr Abbass Adeyemi ne bayan sabon kwamishinan yan sandan jihar ya yi umurnin gudanar da sabon bincike kan duk wasu lamura da suka yi kwantai
  • Bincike ya kai jami'an tsaro ofishin likitan inda suka lura an yi sabon siminti sai suka babbare shi, nan take kuwa suka gano gawar mace binne a kasa

Kwara - Jami’an tsaro sun gano gawar wata mata da aka binne a ofishin Dr Abbass Adeyemi, shugaban babban asibitin Kiama.

A cewar yan sanda, an gano gawar matar mai suna Nofisat Halidu a cikin wani rami a asibitin a kan idon mijinta, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsaffin Hotunan Gogarman Mai Garkuwa Da Mutane John Lyon Yana Bikin 'Birthday' A Cikin Banki Sun Bayyana

Ana tuhumar Adeyemi, wanda a yanzu haka yana tsare da hannu a kashe-kashe daban-daban.

Yan sanda
Tashin Hankali: An Gano Gawar Wata Mata a Ofishin Shugaban Wani Babban Asibitin Arewa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A watan jiya ne rundunar yan sandan jihar Edo ta damke Adeyemi kan kisan wani direban tasi mai suna Emmanuel Yobo Agbovinuere.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana zargin likitan wanda ya fito daga karamar hukumar Offa ta jihar Kwara da kisan direban a ranar 3 ga watan Satumba a Benin sannan ya jefar da gawarsa a garin Otofure da ke babban titin Benin-Lagas.

An tattaro cewa likitan, wanda ya kammala karatunsa a jami’ar Ilorin a 2013, ya hadu ne da marigayi Agbovinuere a watan Yulin 2022 a wani otel sannan ya sa shi aiki.

Sai dai kuma, sabon kwamishinan yan sandan jihar Kwara, Paul Odama, ya bayar da umurnin gudanar da sabon bincike a kan lamarin Halidu.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Kakakin yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okansami, ya bayyana cewa a yayin binciken ne aka gano wannan ci gaban.

Wani bangare na jawabin na cewa:

“Da zuwansa kwamishinan yan sandan ya bayar da umurnin kafa tawagar bincike karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan yan sanda a jihar, don gano abubuwan da ke kewaye da batun sace mutane da sauran lamuran da ba a magance ba kafin zuwansa ofis.
“Bisa umurnin kwamishinan yan sanda, an bude sabon bincike kan lamarin a jiya 30/9/2022. Da ake aiki kan bayanin da wani Dr Adio Adeyemi Adebowale ya bayar a jihar Edo inda yake tabbatar da ya kashe wata Ifeoluwa budurwarsa wacce aka ayyana batanta a yankin Tanke na Ilorin a 2021 da kuma gano gawarta daba bisani a wani jeji da ke yankin Alapa na Ilorin inda a nan ne ya yasar da shi.”

Channels TV ta rahoto cewa rundunar yan sandan jihar ta gayyaci Adebowale kuma a yanzu yana fuskantar shari’a a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

An Yi Arangama Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kalare A Gombe, Wasu Sun Jikkata

Da yake amsa tambayoyi, wanda ake zargin yace ya kashe matashiyar, Ifeoluwa, wacce ya bayyana a matsayin budurwarsa sannan ya jefar da gawarta a wani jeji da ke Alapa, karamar hukumar Asa ta jihar Kwara kafin daga bisa abun ya kai ofishinsa.

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa bincike daban-daban da aka gudanar ya jagoranci jami’an tsaro zuwa ofishin wanda ake zargin a babban asibitin Kaima.

Da zuwan su, jami’an yan sanda sun gano sabon siminti a ofishinsa lamarin da yasa suka yi zargin akwai lauje cikin nadi, sai suka banbare simintin.

Tawagar yan sanda da mutanen da ke wajen sun cika da mamaki bayan gano gawar tsohuwar budurwar shugaban asbitin, Ifeoluwa binne a cikin ofishin nasa bayan an banbare simintin.

Kayayyakin da aka samo a ofishin likitan sun hada da wayoyin hannu guda biyu a cikin jakar matar a cikin wata durowa.

Hakazalika an gano jakunkunan mata guda biyu, gashin kai na kanti, mayafi da kuma yan kanfan mata.

Kara karanta wannan

An kama fasto a jihar Arewa bisa bude asibiti a cocinsa, yana ba da maganin bindiga

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Basarake Mai Martaba Da Matarsa A Jihar Arewa

A wani labarin, tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake a jihar Kwara tare da matarsa da kuma direbansa a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba.

Lamarin ya afku da misalin karfe 4:45 na yamma a Owa-Onire, karamar hukumar Ifelodun, jaridar The Nation ta rahoto.

Basaraken da aka sace mai suna AbdulRahman Fabiyi ya kasance Onire na Owa-Onire.

Asali: Legit.ng

Online view pixel