'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Basarake Mai Martaba Da Matarsa A Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Basarake Mai Martaba Da Matarsa A Jihar Arewa

  • Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani babban basarake a jihar Kwara
  • Maharan sun sace basaraken mai suna AbdulRahman Fabiyi tare da matarsa da kuma direbansa
  • Rundunar yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace an ceto matar basaraken sannan ana kokarin kubutar da sauran

Kwara - Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake a jihar Kwara tare da matarsa da kuma direbansa a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba.

Lamarin ya afku da misalin karfe 4:45 na yamma a Owa-Onire, karamar hukumar Ifelodun, jaridar The Nation ta rahoto.

Basaraken da aka sace mai suna AbdulRahman Fabiyi ya kasance Onire na Owa-Onire.

Kara karanta wannan

An gano wata maboyar 'yan bindiga a Arewa, an fatattaki tsageru, an ceto mutanen da aka sace

Yan bindiga
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Babban Basarake Mai Martaba da Matarsa a Jihar Arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jaridar PM News ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwa al’amarin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Okasanmi ya ce:

“Rundunar yan sandan ta samu labari a ranar 1 ga watan Oktoban 2022 cewa wasu tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken Owa Onire wani gari da ke karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, tare da maarsa da direbansa.
“Tawagar yan sanda tare da yan sa-kai da kuma maharba sun shiga yankin bisa umurnin da aka basu na ceto mutanen da kuma kamo miyagun.
“Kokarin tawagar ya yi sanadiyar ceto matar basaraken da aka sake yayin da aka kama mutum biyu da ake zargin suna da hannu a sace sun Bello Abubakar mai shekaru 31 da Bawa Seketri mai shekaru 30 kuma suna taimakawa rundunar a bincikenta.”

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

A karshe ya kuma bayyana cewa ana nan ana giudanar da bincike domin ceto basaraken da direbansa yayin da aka sada matar da iyalinta.

'Yan Banga Sun Tarfa 'Yan Bindiga A Wata Jahar Arewa, Sun Hallaka 31

A wani labari na daban, kungiyoyin yan banga sun kashe ‘yan bindiga 31 a garin Kanoma da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Talata.

Ku tuna cewa a ranar Lahadi da ya gabata, yan bindiga sun farmaki garin inda suka kashe mutane uku da kuma sace masu jego takwas.

Wani haifaffen garin, Abubakar Ibrahim, ya sanar da jaridar Punch cewa maharan da suka farmaki garin a ranar Lahadi da ya gabata sun yi shirin kai sabon hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel