Rikici A Jam'iyyar APC: Abdullahi Adamu Ya Tuhumci Tinubu Da Yaudara

Rikici A Jam'iyyar APC: Abdullahi Adamu Ya Tuhumci Tinubu Da Yaudara

  • Da alamun jam'iyyar APC na gab da shiga irin rikicin da ya karade jam'iyyar adawa ta PDP
  • Shugaban uwar jam'iyyar APC ya tuhumci Asiwaju Bola Tinubu da kokarin mayar da su saniyar ware
  • Hukumar Zabe ta INEC ta amince jam'iyyun siyasa su fara yakin neman zabe daga jiya Laraba

Abuja - Rikicin da ya biyo bayan sakin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC ya dau sabon salo.

Shugaban uwar jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya aike wasikar kar-ta-kwana wa dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, rahoton Vanguard.

A wasikar da Adamu ya aike cikin dare, ya tuhumci Tinubu da saba alkawarin da yayi da mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar game da mukaman kwamitin yakin neman zaben.

Kara karanta wannan

An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

Adamu
Rikici A Jam'iyyar APC: Abdullahi Adamu Ya Tuhumci Tinubu Da Yaudara Hoto: APC
Asali: UGC

Abdullahi Adamu yace alkawarin da akayi shine a nada shi matsayin mataimakin shugaban kwamitin; a nada Sanata Abubakar Kyari matsayin jagoran Arewa, sannan Hon Emma Eneukwu matsayin jagoran kamfen na Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika a nada Sakataren APC, Iyiola Omisore matsayin mataimakin kwamitin (lamuran jam'iyya); Sakataren shirye-shirye Alhaji Sulaiman Argungu matsayin Jagoran shirye-shiryen kamfe, Hon Victor Giadom matsayin jagoran kamfe na yankin Kudu maso kudu, dss.

Amma lokacin da aka saki jerin sunayen mambobin kwamitin, gaba daya an canza tsarin, riwayar Punch.

Kalaman wasikar

Wannan wasika ta zama wajibi dubi ga abubuwan da suka faru kwanakin nan game da nadin mukaman kwamitin yakin neman zabe inda wasu mambobi suka saki jerin sunayen ba tare da izinin uwar jamiyya ba."
"Mun yi mamakin yadda aka saki sunayen mambobin kwamitin a ranar 23 ga Satumba 2022. Wannan ya sabawa ka'idojinmu da yarjejniyar da Ni da Kai muka yi kan yadda za'a tsara kwamitin da shugabanninta."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

"Idan muka bari aka samu rabuwan kai cikin jam'iyyar, hakan zai kashe kuzarin kamfen kuma zai batawa yan jam'iyyar rai."
"Hakazalika hakan zai baiwa yan adawa daman cin zaben a bulus."

Tinubu ya shilla kasar waje

A lokacin da Atiku ya kaddamar da kwamtin neman zabe, ‘dan takaran jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya tafi kasar waje.

Jam’iyyar APC ta dakatar da soma aikin kamfe, sannan tace za ta fadada kwamitin yakin zaben shugaban kasa wanda yake kunshe da mutum 422.

Asali: Legit.ng

Online view pixel