Cututtuka 9 da Ganyen Gwanda ke kawarwa a jikin dan Adam

Cututtuka 9 da Ganyen Gwanda ke kawarwa a jikin dan Adam

Da yawan mutane su na da masaniyar amfani gwanda ga lafiyar su, sai dai 'yan kalilan ne suke da ilimi akan alfanin ganyen itaciyar Gwanda. Ganyen gwanda ya na dauke da sunadarai dake kawar da cututtuka irin su ciwon daji da makamantan su.

Wani bincike ya bayyana cewa, ganyen gwanda yana dauke da sunadarai irin su phytonutrients, dake habaka tafarkin rayuwar gami da bunkasa ta gudanar jini a jikin dan Adam.

Cututtuka 9 da Ganyen Gwanda ke kawarwa a jikin dan Adam
Cututtuka 9 da Ganyen Gwanda ke kawarwa a jikin dan Adam

Ganyen gwanda yana kunshe da sunadarai da suka hadar da; papain, alkaloid da kuma sunadarin chymopapain dake taka muhimmiyar rawar gani wajen dakile cutar kansa a jikin dan Adam.

KARANTA KUMA: Jerin Mawaka 10 da suka fi kowa kudi a duniya

A sakamakon arziki na wannan sunadarai, Legit.ng ta kawo muku jerin hanyoyin lafiya 9 da ruwan ganyen Gwanda ke ingantawa a jikin dan Adam.

1. Azurta jikin dan Adam da wadataccen jini.

2. Inganta lafiyar hantar dan Adam.

3. Inganta garkuwar jiki mai yaki da kwayoyin cututtuka irin su bacteria da Virus masu sanyan cutar Daji, zazzabin cizon sauro da makamantan su.

4. Cire kasala tare da karfafa gabobi da lakar jikin dan Adam.

5. Saukaka narkewar abinci da kuma tace shi daga cututtuka.

6. Hana kumburin jiki.

7. Inganta lafiyar zuciya tare da ba ta kariyar cututtuka.

8. Hana kamuwa da ciwon sukari ta hanyar daidaiton sundarin Insulin a jikin dan Adam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel