Shugaba Buhari Ya Baiwa Yan Wasan Gudu Kyautar N200m Da Lambar Yabo

Shugaba Buhari Ya Baiwa Yan Wasan Gudu Kyautar N200m Da Lambar Yabo

  • Wadanda suka wakilci Najeriya a gasar wasanni na Commonwealth sun samu babbar kyauta daga wajen Shugaba Buhari
  • Shugaban kasa ya shirya musu taron mika godiya bisa kokarin da suka yi a wasannan na atisaye
  • Yan wasan sun samu lambar yabo kuma da kyautar makudan miliyoyin Naira

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya sanar da kyautar N200 million ga yan wasan gudun Najeriya da suka yi nasara a gasar gudun duniya a kasar Ingila.

Hakazalika shugaban kasa ya baiwa Tobi Amusan, macen da ta karya tarihi a wasar gudun na kasashen Commonwealth 2022 lambar yabo.

Buhari ya karbi bakuncinsu a fadar Aso Villa ranar Alhamis.

Buhari
Shugaba Buhari Ya Baiwa Yan Wasan Gudu Kyautar N200m Da Lambar Yabo Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Jana'izarsa Mambobinsu 26 Da Soji Suka Kashe

Yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wakilan Najeriya a wasannin Commonwealth da ya guda a Birmingham, UK yau a fadar shugaban kasa, Abuja."

Asali: Legit.ng

Online view pixel