Buhari Ya Amince a Kashe N28bn Don Yin Tinubu da Sauran Ababen More Rayuwa a Abuja

Buhari Ya Amince a Kashe N28bn Don Yin Tinubu da Sauran Ababen More Rayuwa a Abuja

  • Gwamnatin Buhari ta amince da kashe makudan kudade domin yin wasu ayyuka a babban binrin tarayya Abuja
  • Hakazalika, za a yi aikin wasu tituna a jihar Bayelsa, musamman a yankunan da ake aikin iskar gas
  • Gwamnatin tarayya ta ce nan da watan Disamban bana za a kammala aikin matatar mai ta Fatakwal

FCT, Abuja - Majalisar zartaswa ta FEC amince a kashe Naira biliyan 28 don gina tituna da sauran ababen more rayuwa a gundumar Wasa dake babban birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.

Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron FEC na ranar yau Laraba 14 ga watan Satumba da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Buhari ya amince da gina sabbin tituna a Abuja
Buhari Ya Amince a Kashe N28bn Don Gyara Babban Birnin Tarayya Abuja | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, ya gabatar da batun kashe N28, 117,904,027, da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi a taron.

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

Ya kuma shaida cewa, a shekarar 2014 da aka fara gabatar da bukatar, an kuduri lashe N56bn, lamarin da yasa ba a yi aikin ba saboda hauhawar farashin kayayyaki da sauran batutuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, an sake duba ga da bukatar ayyukan, kuma shugaban kasa ya amince da kashe N28, 117,904,027.

Ministan ya kuma kara da cewa an kara wa’adin kammala kwangilar zuwa watanni 42, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

An amince da wasu ayyukan a jihar Kudu

Karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, wanda shi ma ya zanta da manema labarai ya ce FEC ta amince da kashe N2.044bn don gina tituna a yankin mai na jihar Bayelsa.

Ministan ya kara da cewa za a kammala matatar mai ta Fatakwal domin ci gaba da hako mai nan da zuwa watan Disamba na wannan shekara.

Kara karanta wannan

Atiku ya sha alwashin yin abin da Buhari ya gaza idan aka zabe shi a 2023

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai wadanda su ya kamata su ke tallata nasarorin da gwamnatinsa ta samu, amma sam ba sa yin hakan, TheCable ta ruwaito.

Buhari ya bayyana haka ne a yau Talata 13 ga watan Satumba a wata ziyarar bude ayyuka da ya kai jihar Imo ta kudancin Najeriya.

Shugaban ya ce, idan aka yi duba cikin tsanaki da irin albarkatun kasa da gwamnatinsa ta samu, za a fahimci irin kokarin da ya yi a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.