Ta Musamman Ce: Bidiyon Yarinya Mai Wani Nau'in Tabon Haihuwa Ya Bar Jama'a Baki Bude

Ta Musamman Ce: Bidiyon Yarinya Mai Wani Nau'in Tabon Haihuwa Ya Bar Jama'a Baki Bude

  • Wani hadadden bidiyo na wata kyakkyawar yarinya dauke da tabon haihuwa da farin gashi a goshinta ya yadu a shafukan soshiyal midiya
  • Bidiyoyi da dama da aka wallafa a TikTok Ya nuno karamar yarinyar cikin kwalliya iri-iri tana mai nuna baiwar da Allah ya yi mata
  • Da suke martani ga bidiyoyin, jama’a sun nuna mamakinsu, inda da dama suka jadadda irin baiwar da yarinyar ke dauke da shi

Wata karamar yarinya ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya saboda kyawun halitta irin nata, tana dauke da wani tabon haihuwa mai matukar haske a goshinta.

Allah ya yiwa kyakkyawar yarinyar wata baiwa da ba a saba gani ba a fuskanta wanda ya sace zukatan jama’a inda suka jinjina mata.

Karamar yarinya
Yar Baiwa: Bidiyon Karamar Yarinya Da Aka Haifa Dauke Da Haske Da Furfura A Goshinta Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@tasharuth00
Asali: UGC

A bidiyoyi da dama da mahaifiyarta mai suna @tasharuth00 ta wallafa a TikTok, kyakkyawar yarinyar ta baje wannan tabo nata yayin da take rera waka mai dadin sauraro.

Kara karanta wannan

Ruwan dare: Budurwa ta jawo cece-kuce yayin da ta kammala digiri, tace za ta rushe gidansu

Wasu bidiyoyi da aka gano a shafin ya nuna tabon haihuwa mai matukar haske da kyalli da yarinyar ke dauke da shi da kuma furfura a goshinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama’a sun mato a kan yarinyar

Yayin da wasu suka kirata da yar baiwa, wasu sun nuna mamakinsu kan yanayin halittarta wanda ba kasafai ake samun irinsa ba.

@jeremiahujerekre1 ta ce:

“Wato iyayen yarinyar suna da masaniya cewa sun haifi yar baiwa ce a fuskar mutum. Na taba ganin irin haka..mutane ne na musamman.”

@user3857607215165 ta rubuta:

“Kyakkyawar hallitar Allah, dan Allah kada ki yi kokarin canja shi. Irin wannan tabarraki ne da Allah da kansa ya halicce shi. Idan kika fara kasuwanci, ki bari ta saka albarka.”

@whatisthisdayle ta ce:

“Zuwa ka iyayenta, na roke ku da ku bata kariya kuma dan Allah kada ku wallafa hotunanta. An baku kyauta, dan Allah ku kareta da kauna tana da muhimmanci.”

Kara karanta wannan

Ina Mai Rokonka Dan Allah, Ka Kula Da Diyata: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Ya Roki Surukinsa A Bidiyo

Kalli bidiyon a kasa:

Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Kan Bidiyonsa

A wani labari makamancin wannan, bidiyon wani karamin yaro bakin fata dauke da idanu masu launin shudi da wasu hallita ta musamman ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya.

A cikin wani bidiyon TikTok da ya samu sama da mutane miliyan daya da suka kalla, yaron ya kalli cikin kamara yayin da aka hasko yanayin halittar fuskarsa mai ban mamaki.

Baya ga idanu masu launin shudi da yaron ke dauke da su, yana kuma da furfura a gaban gashin kansa sannan akwai wani fashin haske kamar na tsawa shimfide a fuskarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel