Layin Fetur Na Shirin Dawowa, ‘Yan Kasuwa Sun Tafi Yajin-aiki Saboda Bashin N50bn

Layin Fetur Na Shirin Dawowa, ‘Yan Kasuwa Sun Tafi Yajin-aiki Saboda Bashin N50bn

  • Kungiyar Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria watau IPMAN ta soma yajin-aiki daga ranar Litinin a Najeriya
  • ‘Yan kasuwa sun ce akwai tulin kudinsu a hannun Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority
  • Za a cigaba da saida fetur a gidajen mai, amma babu wata babbar mota da za ta dauko mai daga tashoshin Legas zuwa jihohin Arewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Alamu na nuna za a iya shiga wani sabon wahalar man fetur a dalilin yajin-aikin kwana uku da kungiyar ‘yan kasuwa suka shiga daga jiya.

A ranar Litinin, 5 ga watan Satumba 2022, ‘yan kimgiyar IPMAN suka soma yajin-aiki a dalilin bashin N50bn, Daily Trust ta fitar da wannan labari.

Shugaban kungiyar IPMAN na reshen Suleja a jihar Neja, Alhaji Yahaya Alhassan ya shaida cewa hukumar NMDPRA ta gagara biyansu hakkokinsu.

Kara karanta wannan

Hotuna: Lamiɗo, Da Wasu Yan Takarar Gwamna 16 Na Jam'iyar PDP Sun Sa Labule da Wike

Yahaya Alhassan yace tun watan Junairu rabon da hukumar ta biya su alawus na dakon fetur da suka yi daga tasoshin Legas zuwa jihohin Arewa.

‘Yan kungiyar ta IPMAN suna dauar mai daga Legas zuwa tashohi a Borno, Adamawa, Kano, Kaduna, Benuwai, Filato, Gombe, Neja da Zamfara.

Rahoton da Punch ta fitar yace motocin man da suka dauko fetur daga Legas suna nan a jibge a Suleja, sun fara yajin-aiki na tsawon kwanaki uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Layin Fetur
Wani Gidan mai a Najeriya Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Kungiyar ta IPMAN tana zargin shugaban NMDPRA da kin biyansu kudinsu wanda ya kai N50.6bn, hakan ya jawo suka janye aikin da suka saba yi.

“Muna da hujjar cewa mun shigo da mai, muna bin su N50.5bn. Sun fara biyan kudin daga lokacin da hukumar ta canza suna zuwa NMDPRA.
Amma tun Disamban 2021, ba su biya mu ba, mutanenmu sun fara hakura da kasuwancin.”

Kara karanta wannan

Mun gane kuskurenmu: Wasu ‘Yan daban Siyasa Sun Ajiye Makamai, Sun Shiga APC

- Yahaya Alhassan

Za a samu fetur a gidajen mai?

Alhaji Musa Yahaya Mai Kifi wanda shi ne shugaban kungiyar NIPMF yace za a cigaba da saida fetur a gidajen mai, amma babu motar man da za ta bar Legas.

IPMAN ta reshen jihar Borno tace kudin da take bin gwamnati ya kai N70bn. Kakakin kungiyar, Abdulkadir Mustapha yace NMDPRA sun rike masu dukiya.

Kokarin Isa Ali Pantami

A baya kun samu labarin yadda Isa Ali Pantami ya tsaya tsayin daka, ya aikawa shugaban Najeriya takardar korafi cewa ka da a kara haraji a harkar sadarwa.

Ministan ya nunawa Muhammadu Buhari idan aka shigo da haraji, an kara jefa al’umma da tattalin arziki a matsala, wannan ya sa aka fasa kara farashin waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel