Kasar Saudiyya Ta Fara Bincike Kan Wani Bidiyon Yadda Jami’an Tsaro Suka Zane Wasu Mata

Kasar Saudiyya Ta Fara Bincike Kan Wani Bidiyon Yadda Jami’an Tsaro Suka Zane Wasu Mata

  • Wani bidiyo ya nuna lokacin da wasu jami'an tsaro a kasar Saudiyya ke lakadar wasu 'yan mata a gidan marayu
  • Bidiyon ya tada hankali, lamarin da ya ja gwamnatin kasar ta fara bincike don gano tushe da sababin dukan
  • Gwamnatin Saudiyya ta ce bata san dalilin yin wannan duka ba, kana za ta tabbatar da ba bayanan sakamakon binciken

Saudiyya - A ranar Laraba ne hukumomin Saudiyya suka fara bincike kan wani faifan bidiyo dake yawo da ya nuna yadda wasu jami’an tsaro ke dukan 'yan mata a gidan marayu da ke Kudu maso Yammacin kasar.

Arab News ta ruwaito cewa, gwamnan yankin Asir ya hada wani kwamiti da zai binciki dukan da aka gani yana yawo a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

Bidiyon yadda aka daka wasu a gidan marayun Saudiyya
Kasar Saudiyya Ta Fara Bincike Kan Wani Bidiyon Yadda Jami’an Tsaro Suka Zane Wasu Mata | Hoto: arabnews.com
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana halin da lamarin da ya faru na lokacin da aka dauki bidiyon da kuma dalilin dukan ba.

A faifan bidiyon, alamu sun nuna an dauki bidiyon ne a gidan marayu dake birnin Khamis Mushat.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ga wasu mata sanye da bakaken kaya yayin da wasu jami'ai ke rike dasu suna lakadarsu da bulalin fata da katako.

An ga wani jami'i na jan gashin wata mata kana yana jan ta a kasa tana kururuwa. Wani faifan bidiyo kuma ya nuna yadda jami’an ke kora 'yan matan a gidan marayu.

Bidiyon da ya yadu a kafar Twitter tare da lakanin KhamisMushaitOrphans ya jawo cece-kuce daga mutane da dama, rahoton Washington Post.

Yunwa da Wahala Ta Kashe Sabbin Sojojin Kudancin Sudan Sama da 200

A wani labarin, iftila'i ya faru a sansanin horar da sojojin Kudancin Sudan yayin da wasu sojoji sama da 200 suka mutu a atisayen horo kafin su kai ga rukunin yaye, a cewar mataimakin shugaban kasa nafarko, Riek Machar a jiya Talata 30 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Yan Uwansa Sun Cika Alkawari: Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Dan Najeriya Mazaunin Dubai Ya Ja Hankali

Mataimakin shugaban kasa Machar ya ce sojojin sun jarabtu da azababben sauyin yanayi ne da dai sauran cututtuka a lokacin da yake jawabi yayin bikin yaye sojojin a Juba, babban birnin kasar.

A cewarsa: “Na san abokanku sama da 200 ne suka rasa rayukansu a cibiyoyin horo 18 – wasu cututtuka ne suka kashe su kasancewar babu magani, wasu kuma sun mutu ne saboda yunwa sakamakon rashin abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel