Yunwa da Wahala Ta Kashe Sabbin Sojojin Kudancin Sudan Sama da 200

Yunwa da Wahala Ta Kashe Sabbin Sojojin Kudancin Sudan Sama da 200

  • An yaye jami'an sojin kasar Kudancin Sudan, gwamnatii ta bayyana adadin mutanen da suka mutu yayin horo
  • Cututtuka daban-daban ne suka hallaka sojoji, hakazalika yunwa da rashin isasshen abinci ya hallaka da dama
  • Wasu daga cikin sojojin da aka yaye tsoffin mambobin kungiyoyin 'yan tawaye ne da suka addabi a kasar a baya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Juba, Kudancin Sudan - Iftila'i ya faru a sansanin horar da sojojin Kudancin Sudan yayin da wasu sojoji sama da 200 suka mutu a atisayen horo kafin su kai ga rukunin yaye, a cewar mataimakin shugaban kasa nafarko, Riek Machar a jiya Talata 30 ga watan Agusta.

Mataimakin shugaban kasa Machar ya ce sojojin sun jarabtu da azababben sauyin yanayi ne da dai sauran cututtuka a lokacin da yake jawabi yayin bikin yaye sojojin a Juba, babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Wani abu zai faru, gwamnati ya share ASUU, ta kira ganawa da shugabannin jami'o'i

Akasarin sojojin da suka mutu sun fito ne daga tsoffin kungiyoyin tawayen SPLA-IO da kuma SSOA, kamar yadda BBC News ta ruwaito.

Cututtuka da yunwa sun kashe sojojin Sudan
Yunwa da Wahala Ta Kashe Sabbin Sojojin Kudancin Sudan Sama da 200 | Hoto: clubofmozambique.com
Asali: UGC

A cewarsa lokacin da yake jawabi:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Na san abokanku sama da 200 ne suka rasa rayukansu a cibiyoyin horo 18 – wasu cututtuka ne suka kashe su kasancewar babu magani, wasu kuma sun mutu ne saboda yunwa sakamakon rashin abinci.
"A yau ina taya ku murna bisa juriya da jajircewa da kuka nuna."

Ranar da aka dade ana jira

Ya kuma bayyana cewa, wnanan biki ne da 'yan kasar suka dade suna jira, domin ba da kwarin gwiwa ga miliyoyin 'yan gudun hijiran da suka tsallake kasar zuwa kasashen makwabta su dawo gida.

A cewar jawaban gwamnati a yayin biki, sama da sojoji 22,000 ne aka yaye daga cibiyoyin horar da jami'ai daban-daban a kasar.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya fadi abin da gwamnati za ta yi

Wadannan rundunoni dai su ne sojan kasa na farko da suka kunshe kalubu mabambanta a Kudancin Sudan.

Sai dai, wani rahoton DailyItem ya ce, an yaye sojojin ne ba tare da bindigar gaske ba, inda aka gansu dauke bindigogin katako.

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

A wani labarin, rahoto daga jaridar Punch ya ce, shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya ce a ko da yaushe Najeriya a shirye take ta ba Jamhuriyar Sudan ta Kudu taimako don samun kwanciyar hankali na siyasa da tattalin arziki.

Ya bayyana haka ne yayin da yake nuna damuwarsa game da rashin kwanciyar hankali na siyasa a Libya, yana mai cewa muddin kasar ba ta da kwanciyar hankali, yaduwar makamai da manyan makamai a yankin Sahel zai ci gaba.

Buhari ya fadi haka ne a ranar Talata 5 ga watan Oktoba a Addis Ababa yayin ganawar bangarorin biyu da Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu, inji PM News.

Kara karanta wannan

Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

Asali: Legit.ng

Online view pixel