Kowa da Irin Nasa Kokarin, Shugaba Buhari Ya Yi Iyakar Kokarinsa, Inji Isa Yuguda

Kowa da Irin Nasa Kokarin, Shugaba Buhari Ya Yi Iyakar Kokarinsa, Inji Isa Yuguda

  • Tsohon gwamnan jihar Bauchi ya bayyana irin kokarin da shugaba Buhari ya yi a kokarinsa na yakar matsalar tsaro
  • Isa Yuguda ya yi imanin cewa, bai kamata a kakaba laifin matsalar tsaro a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba
  • Dan majalisar wakilai ya dage shi ma lallai Buhari ya yi kokari, kuma bai kamata a daura masa laifi ba

Najeriya - Yayin da'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa game da mulkin Buhari, tsohon gwamnan Bauchi ya yaba da irin kokarin da Buhari ya yi shekarun mulkinsa.

Ya bayyana yabonsa ne ga Buhari a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily.

Isa Yuguda, ya ce shugaba Buhari ya yi iyakar kokarinsa idan aka yi duba da lamurran tsaro da kuma kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Alhassan Doguwa: Matsalar tsaro ba laifin Buhari bane, ya ma kare 'yan Najeriya ne

Buhari ya yi iyakar kokarinsa, inji tsohon gwamnan Bauchi
Buhari ya yi iya kokarin sa, kowa da irin nasa kokarin, inji Isa Yuguda | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Isa Yuguda dai tsohon ministan sufurin jiragen sama ne a Najeriya, kuma ya yi gwamna a jihar Bauchi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Shugaban kasa dai ya yi iya kokarinsa. Kowa da irin kokarinsa, kuma ya bambanta. Don haka zan iya cewa shugaban kasa ya yi iyakar kokarinsa.
“Kuma ya nada kwararrun da za su taimaka masa wajen tafiyar da kasar nan - su ma din suna iyakar kokarinsu. Ya danganta da yadda aka kimanta kokarin. A iya fahimtata, shugaban kasa ya yi iyakar kokarinsa.”

Lokacin da aka titsiyeshi ya yi karin bayani game fahimtar tasa.

Isa Yuguda ya amince akwai kalubale a harkar tsaron Najeriya, amma duk da haka ya dage Buhari ya yi matukar kokari.

Duk mai hankali yasan Buhari ya kokari

Channels Tv ta ruwaito shi yana cewa:

"Duk wani dan Najeriya mai tunani ya sani cewa lamura ba za su kyau ba ko da kuwa wanene ke jan ragamar kasar.

Kara karanta wannan

Buhari: Abin Da Yasa Ba Za Mu Iya Kara Wa Ma'aikata Albashi Ba Duk Da Ya Kamata

“Mafi yawan wadannan abubuwan da ke faruwa da mu a kasar nan dogon tarihi ne.
“Idan ka fito daga al'ummar da take gurbatacciyar tun daga tushe, to abin da ka shuka tabbas shi za ka girba.
“Batun tsaro, misali, abu ne na dogon tarihi. Ba a zamanin Buhari aka fara ba. Lamarin ya fara ne a 2008, 2009."

Daga karshe, Yuguda ya sake jaddada cewa, bai kamata 'yan Najeriya suke daura laifin kalubalen tsaron Najeriya a kan shugaba Buhari ba.

Buhari Ya Yi Matukar Kokari Wajen Kare ’Yan Najeriya Da Dukiyoyinsu, Inji Alhassan Doguwa

A wani labarin, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yaba da irin kokarin da shugaba Buhari ya yi na kare 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Doguwa ya dage cewa, tsaro aiki ne na kowa, kuma shugaba Buhari ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin bai gaza kare 'yan kasarsa ba.

Kara karanta wannan

'Zan Fitar Da Najeriya Daga Duhu', Atiku Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Bangaren Lantarki

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi 22 ga watan Agusta a jihar Kano yayin wani aron karrama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel