'Yan Sanda Sun Cafke Mutum 5 da Ake Zargin Sun Farmaki Tawagar Uwar Gidan Gwamnan Osun

'Yan Sanda Sun Cafke Mutum 5 da Ake Zargin Sun Farmaki Tawagar Uwar Gidan Gwamnan Osun

  • Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta tabbatar da kai farmaki kan ayarin motocin uwar gidan gwamnan jihar
  • An kama wasu matasa biyar da ake zargin suna da hannu a jifan motocin uwar gidan gwamnan Osun a ranar Juma'a 19 ga watan Agusta
  • Rahotanni a baya sun bayyana yadda wasu matasa suka yi wa ayarin uwar gidan gwamna ba dadi a jihar Kudu

Jihar Osun - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, rundunar an kame wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a farmakar tawagar uwar gidan gwamnan Osun.

A yau Asabar 20 ga watan Agusta ne rundunar 'yan sandan jihar Osun ta tabbatar da an kai farmaki kan ayarin motocin uwar gidan gwamnan jihar, Misis Kafayat Oyetola a jiya Juma'a a Owode na yankin Ede.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Matar Gwamna Mummunan Farmaki

Wata sanarwa da rundunar ta fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunta, SP Yesimi Opalola ta bayyana cewa, jami'in tsaro daya ya raunata a harin.

Yadda 'yan sanda suka kame mutanen da suka farmaki matar gwamna
'Yan Sanda Sun Cafke Mutum 5 da Ake Zargin Sun Farmaki Tawagar Matar Gwamnan Osun | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Wani yankin sanarwar na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A ranar Juma’a, da wajajen karfe 8:30 na dare, ‘yan sanda sun samu rahoton cewa, wasu ‘yan bindiga sun farmaki ayarin motocin uwar gidan gwamnan Osun a Owode, babban titin kasuwar Ede.
“Cikin gaggawa jami’in ‘yan sandan yankin ‘A’ a Ede, ya tattara jami'an bincike ya jagorance su zuwa wurin da lamarin ya faru, inda tawagar ta tarar da CSP Dauda Ismail, babban jami’in tsaron gwamna Gboyega Oyetola na Osun."

Yadda lamarin ya faru daga bakin jami'an 'yan sanda

Da yake karin haske game da yadda lamarin ya faru, SP Yesimi ya bayanin cewa, wani direban babbar mota da ke gaban ayarin uwar gidan gwamnan ne ya tsohe hanya, lamarin da ya kawo tsaiko.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe fitaccen lauya a Zamfara

Ya kuma cewa, an raunata direban babbar motar da kuma wani jami'in DSS da ke tare da ayarin, Daily Sun ta ruwaito.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“CSP Ismail ya shaidawa wa rundunar cewa, wani mai suna Omolola Opeyemi, direban Ijebu-Ode a jihar Ogun, ya tuko babbar mota da ba ta da rijista kana ya toshe hanyar Oyetola.
“Sakamakon cunkoson da aka samu, wasu tsageru sun yi amfani da wannan damar wajen jifa kan ayarin motocin uwar gidan gwamnan, inda suka raunata direban babbar motar a goshi kana suka raunata wani jami’in DSS.
“Sai dai, an kama mutum biyar a wurin kuma ana ci gaba da bincike akansu."

Rundunar ta bayyana cewa, za ta tuntubi manema labarai bayan kammala bincike.

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Matar Gwamna Mummunan Farmaki

A wani labarin, a yammacin Juma'a, wasu da ake zargin miyagun 'yan bindiga ne sun kai wa tawagar uwargidan gwamnan jihar Osun, Kafayat Oyetola, mummunan farmaki, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Rikakken 'Dan Bindiga Lawal Kwalba, Sun Kwato Kayan Hada Bama-bamai

Duk da har yanzu babu bayanai masu yawa kan harin, majiyoyi a Owode dake Ede, inda lamarin ya auku sun ce tawagar matar gwamnan ta nufi Osogbo ne kuma wurin kasuwar Owode 'yan bindigan suka bude mata wuta wurin karfe 8 na dare.

Wani mazaunin yankin wanda ya bayyana sunansa da Alayande, ya sanar da jaridar Punch cewa wata babbar mota ce ta samar da cunkoso lokacin da tawagar matar gwamnan ta isa kasuwar Owode.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.