Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matafiya a Jihar Kwara

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matafiya a Jihar Kwara

  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya shida yayin da suke kan hanyar komawa gida a jihar Kwara
  • Hukumar yan sanda reshen jihar tace dakarunta sun yi nasarar ceto mutum huɗu daga ciki, kuma zasu kubutar da ragowar su kame maharan
  • Kwamishinan yan sandan Kwara ya nemi iyalan sauran su kwantar da hankulan su, ƴan uwansu na kan hanyar dawowa gida

Kwara - Miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane Shida a kan hanyar Obbo-Ile/Osi, a ƙaramar hukumar Eikiti a jihar Kwara yayin da suke kan hanyar koma wa gida daga tafiya.

Daily Trust ta rahoto cewa mutanen da aka sace na kan hanya na cikin wata motar Bas Toyota Hiace bus (Hummer) mai lambar rijista Abuja KUJ 613 AA yayin da tsautsayin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Har Yanzun Akwai Sauran Fasinjojin Jirgin Ƙasa a Hannun Yan Ta'adda, Mamu Ya Faɗi Mummunan Halin Da Suke Ciki

Harin yan bindiga.
Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matafiya a Jihar Kwara Hoto: punchng
Asali: Twitter

Rahoto ya nuna cewa tsagerun yan bindigan sun yi awon gaba da matafiyan ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:15 na dare.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

A halin yanzun wasu bayanai sun nuna cewa haɗakar jami'an tsaro, Sojoji, Yan Banga, da yan sanda sun bazama cikin jeji domin kuɓutar da matafiyan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi (SP), ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Okasanmi, wanda ya faɗi adadin maharan su 5 ɗauke da makamai, ya ce sun gano motar matafiya a yashe gefen titi kuma da bakin harsashi a cikin motar.

A cewarsa, tuni jami'an yan sanda suka kubutar mutum huɗu daga ciki kuma nan ba da jimawa ba zasu ceto ragowar biyun, waɗan ake kyautata zaton suna cikin jeji.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Da Yawa Sun Mutu Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Mummunan Hari Garuruwa Biyu a Jihar Katsina

Kakakin yan sandan ya ce:

"Kwamishinan yan sandan jihar Kwara a ranar Talata ya tabbatar wa iyalan sauran mutanen cewa ba za'a yi ƙasa a guiwa ba wajen kubutar da yan uwansu daga hannun masu garkuwa."

A wani labarin kuma Har yanzun akwai sauran fasinjojin Jirgin Ƙasa a hannun yan ta'adda, Mamu ya faɗi mummunan halin da suke ciki

Tukur Mamu, wanda a baya ya kasance mai shiga tsakani, ya tabbatar da cewa labarin sako ragowar fasinjojin jirgin kasan Kaduna ƙarya ne.

Ɗan jaridan, makusancin Sheikh Ahmad Gumi, ya ce akwai sauran Fasinjoji 27 a cikin jeji kuma suna hali mai matuƙar muni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel