Kamar Almara: Bidiyon Na'urar Daukar Hoto Ta Sama Mai Siffar 'Super Man' Ta Girgiza Intanet

Kamar Almara: Bidiyon Na'urar Daukar Hoto Ta Sama Mai Siffar 'Super Man' Ta Girgiza Intanet

  • Wani bidiyo mai ban sha’awa ya nuno yadda wasu mutane suka saki wata na’ura mai siffar ‘Super Man’ a sama
  • Na’urar ta cilla sama kamar dai yadda ake gani a cikin fina-finan Turai, lamarin da ya jefa mutane a tunanin ko da gaske irin hakan na faruwa
  • An tattaro cewa an dauki bidiyon ne a Brazil, amma ya yadu a manyan shafukan soshiyal midiya ciki harda Facebook da YouTube

Brazil - Wani bidiyon YouTube ya nuno lokacin da aka saki wani na’ura mai siffan ‘superman’ a sama.

A cewar tashar Caters Video, Lauya Everton Marcelo, mai shekaru 40, daga Ribeirao Preto, Brazil ne saki na’urar bayan wasu abokansa sun kera ta.

Superman
Kamar Almara: Bidiyon Na'urar Daukar Hoto Ta Sama Mai Siffar 'Super Man' Ta Girgiza Intanet Hoto: YouTube/ Caters Video.
Asali: UGC

Na’urar ta lula can sama kamar yadda dai ake gani a cikin fina-finan Turai kuma hakan ya matukar bawa mutane mamaki.

Kara karanta wannan

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

Caters Videos ya rahoto cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Abokan Everton sun samar da wata na’ura mai tashi a sama ta hanyar amfani da siffar karamin jirgin sama, injin mai bayar da iska da batir a ciki. Sai aka yi tunanin sauya na’urar zuwa siffar Superman, ta yadda abun ya yi kamar da gaske jarumin na yawo ne a saman garin Brazil.”

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da YouTube sun yi martani

John Smith ya yi martani:

“Dan Allah Dan Allah ku sa shi ya yi yawo a saman birnin sannan ya nadi martanin mutane.”

Emmanuel Olusegun ya yi martani:

“Kuna iya sanya tayoyi a kan kirjinsa don sauka cikin sauki.”

Tony Blay ya ce:

“Fasaha mai kyau amma ya kamata Mista Superman ya iya sauka kan kafafunsa ba wai da kirjinsa ba idan ba haka ba zai zama Mista Chestman.”

Kara karanta wannan

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

Lukasz Dźbik ya yi martani:

“Abun akwai ban dariya sosai kuma ya kayatar.”

Amber Martin ya ce:

“Na so gayen da ke dariya a bidiyon.”

Ana Shagali A Lagas: Bidiyon Dan Achaba Yana Jan Motar Bas Mai Cin Mutum 18 Da Igiya

A wani labarin, jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyana bidiyon wani dan achaba yana jan motar bas mai cin mutane 18.

A cikin bidiyon wanda tuni ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano yadda aka daure motar bas din wacce ga dukkan alamu ta samu matsala ne a jikin babur din da igiya.

Sai direban babur din ya dungi jan motar a kan titi wanda ke dauke da cunkoson ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel