Hotunan Yadda Aka Yi Jana'izar Sojojin Da Yan Ta'adda Suke Kashe A Abuja
1 - tsawon mintuna
- An yi jana'izar dakarun sojojin Najeriya guda biyar na Guards Brigade da wasu yan ta'adda suka halaka su yayin harin kwanton bauna a Abuja
- Yan ta'addan sun halaka dakarun sojojin ne da yayin da suka afka wa tawagarsu a lokacin da suke dawowa daga amsa kirar neman dauki a makarantar horas da lauyoyi
- Manyan jami'an rundunar sojojin Najeriya sun hallarci jana'izar ciki har da kwamandoji, Staff ofisa har ma da shugaban karamar hukumar Bwari, Honn John Gabaya
FCT, Abuja - A ranar Alhamis ne aka birne dakarun sojoji na Guards Brigade da yan ta'adda suka kashe a babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta rahoto.
An birne jagoran sojojin Kyaftin Attah Samuel da wasu sojoji hudu wanda suka sadaukar da rayuwarsu, a makabarta ta Guards Brigade da ke Maitama, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin rasuwarsu, dakarun sojojin suna aiki ne tare da 7 Guards Battalion, Barikin Lungi Maitama da 176 Guards Battalion, Gwagwalada, FCT Abuja.
Ga hotunan yadda aka yi jana'izarsu a kasa:
Asali: Legit.ng