Soyayya gamon jini: Tsoho mai shekaru 93 yayi wuff da budurwarsa mai shekaru 88

Soyayya gamon jini: Tsoho mai shekaru 93 yayi wuff da budurwarsa mai shekaru 88

  • Wasu dattawan ma'aurata 'yan New York sun ki yadda cewa ba zasu samu soyayya ba yayin da suka yi aure bayan sun hadu a yanar gizo
  • Robert Marshall mai shekaru 93 tare da amaryarsa Anne Cooper mai shekaru 88, ta bayyana irin mijin da take so da irin nagartarsa tun tana yarinya
  • Sun hadu a wata manhajar neman abokan rayuwa, dukkansu sun rasa abokan rayuwarsu kuma mijin ya bayyana cewa a ganin farko ya kamu da son ta

Wata amarya da angonta sun tabbatar da cewa, soyayya ruwan zuma ce a yayin da suka daura aure duk da yawan shekarunsa.

Ba su yarda cewa tsufa za ta hana su komai ba, sun nemi abokan rayuwarsu, wadanda zuciyarsu ke kauna da kuma wanda suke fatan kare rayuwarsu da shi.

Kara karanta wannan

Baiwa ce daga Allah: Hoton mata masu tsawon rai da kakar kakarsu ke da rai ya janyo cece-kuce

Masoya
Soyayya gamon jini: Tsoho mai shekaru 93 yayi wuff da budurwarsa mai shekaru 88. Hoto daga people.com
Asali: UGC

Masoyan junan duk da tsofaffi ne, sun bayyana wurin daurin auren rike da hannayen junansu kuma suna bayyana cewa sun samu soyayya a lokacin da basu taba tsammani ba.

Daga matar har mijin duk sun rasa abokan rayuwarsu lokacin da suka yanke hukuncin neman abokan rayuwa a yanar gizo kuma suka yi kira ga dattawa masu neman masoya da kada su sare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ganin farko na fada soyayyarta

Robert ya garzaya manhajar neman masoya kafin ya ci karo da hoton matarsa kuma ya gane cewa ita ce abokiyar rayuwarsa.

Kamar yadda jaridar People ta ruwaito, Anne ta bayyana cewa lokacin farko da ta hadu da Robert domin tattaunawa, ya tsaya cike da izza kuma da yadda ya bayyana, dole ta fada soyayyarsa.

Babu shakka masoyan junan sun bayyana hotunan juna inda suka yi kyau ba kadan ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa

Kano: Wurin rige-rigen shiga gaban mota, amarya ta sumar da uwargida, alkali ya aikata gidan yari

A wani labari na daban, Alkali ya aike da amarya gidan gyaran hali bayan da ta sumar da kishiyarta yayin da suke rige-rigen shiga gaban motar mijinsu. Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, lamarin ya auku a Kano ne a satin da ya wuce.

Uwargida ta sanar da kotun shari'ar dake Kofar Kudun gidan Sarki a gaban Alkali Ibrahim Sarki Yola cewa, kishiyarta ta lakada mata duka.

Uwargidan dake kara tace bata cika lafiya ba, lamarin da yasa mijinsu ya aiko da mota a kai ta asibiti saboda ba za ta iya tuka motarta ba.

Uwargida ta bayyana cewa, tana shiga motar ne amarya ta rike kofa tana ce mata ta fito, inda ita kuwa tace ba za ta fito ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel