Daga shiga rubuta JAMB: An kama wani matashi da ya fece da wayoyi 21 da aka bashi ajiya

Daga shiga rubuta JAMB: An kama wani matashi da ya fece da wayoyi 21 da aka bashi ajiya

  • Jami’an tsaron NSCDC sun kama wani da ake zargi da aikata laifin sata mai suna Quadri Qudus
  • An kama Qudus mai shekaru 23 da laifin satar wayoyi 21 daga masu neman shiga jami'a a Ilorin babban birnin jihar Kwara
  • Ana zarginsa da satar wayoyin ne daga hannun masu neman shiga jami’a a lokacin da suke rubuta jarabawarsu ta kwamfuta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jami’an tsaron NSCSC sun kama wani matashi dan shekara 23 mai suna Quadri Qudus wanda ake zargi da satar wayoyin hannu 21 daga masu neman shiga jami’a a Ilorin babban birnin jihar Kwara, Daily Trust ta ruwaito.

An zargi Quadri da satar wayoyin ne daga hannun masu neman shiga jami’a a lokacin da suke rubuta jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare a wata cibiyar jarrabawa kwamfuta da ke Ilorin a ranar 5 ga Yuli, 2022.

Yadda aka kama barawon wayoyi
Barawon kasa-da-kasa: Wani dan jihar Kwara ya saci wayoyi 21 daga masu rubuta JAMB | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai dai kafin daliban su kammala rubuta jarrabawarsu, wanda ake zargin ya tsere daga cibiyar tare da wayoyin da aka ba shi ajiya, rahoton Tribune Online.

Da yake gabatar da Quadri tare da wasu mutane biyu a hedikwatar NSCDC a ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar, Olasunkanmi Ayeni, ya ce wanda ake zargin ya shiga hannun jami’an, kuma an kama shi ne a Ilorin bayan kusan wata daya da aikata laifin..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayeni ya ce:

“Quadri Qudus ya yi kamar yana sayar da takunkumin fuska a cibiyar jarrabawar JAMB, dalibai kuma saboda ganin sun yarda dashi suka ba shi wayoyin a hannun sa ajiya, amma ya gudu dasu. Daga karshe dai mutanenmu sun kama shi a Ilorin.”

Martanin barawon

Da yake magana da manema labarai, Quadri ya musanta cewa ya gudu da wayoyin yana mai cewa an sace wayar ne kuma ya gudu ne saboda fargabar kama shi da kuma kona shi da masu su wata za su yi.

Ya yi da'awar cewa:

“Da gaske an sace wayoyin ne daga inda na ajiye su. Na gudu don tsoron abin da zai same ni.
"Dole ne na gudu don tsira da raina kafin masu su su fito daga cibiyar jarrabawar saboda za su yi mani dukan tsiya kuma su kona ni idan sun samu labarin cewa an sace musu wayoyin."

An kama wani jami'in 'yan sanda da aka gani bidiyo yana shin karbar cin hanci

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wani dan sanda mai suna Victor Osabuohign aka dauka a wani faifan bidiyo da aka yana ciniki da wani maia bin hawa da nufin karbar kudi a hannunsa.

ASP Jennifer Iwegbu, mataimakiyar jami’in hulda da jama’a na rundunar ne ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a Benin ranar Juma’a, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ms Iwegbu ta ce an kama jami’in, an tsare shi kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike akansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel