Kaduna: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga Bayan Musayar Wuta, Sun Kwato Bindigun AK-47 Da Babura

Kaduna: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga Bayan Musayar Wuta, Sun Kwato Bindigun AK-47 Da Babura

  • Jami'an tsaro a Jihar Kaduna sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan bindiga da ke adabar mutane a Eastern by-pass, karamar humumar Chikun
  • Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yana mai cewa an kwato bindigu, layyu, babura da wayar salula bayan kashe shi
  • Aruwan ya kara da cewa cikin kwanaki biyu da suka shude, jami'an tsaro a jihar sun yi nasarar kama wasu yan bindiga da kuma masu dillancin bindigan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce, a ranar Talata, dakarun sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga da ke adabar matafiya a Easter by-pass, karamar hukumar Chikun na jihar, rahoton The Punch.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an kwato AK-47 biyu, layyu da guraye, wayar salula da babura biyu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

Taswirar Jihar Kaduna
Kaduna: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga, Sun Kwato Bindigun AK-47 Da Babura. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan yana martani ne kan shirin kawo hari da yan bindiga za su yi a Kaduna da kewaye, ya yi kira ga mutane su cigaba da sa ido.

Aruwan ya ce gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na kawo karshen kallubalen tsaro a jihar.

"Bisa kokarin da suke yi, jami'an tsaro a cikin awa 48 da suka shude sun kama wasu yan bindiga da dilallan bindiga a Kidunu, kusa da Eastern by-pass, karamar hukumar Chikun.
"Bayan musayar wuta, an kashe dan bindiga daya, wanda daga baya aka gano hatsabibin dan bindiga ne da ke adabar yankin. An kwato AK-47 biyu, da layyu da guraye, wayan salula da babur," wani sashi na jawabinsa.

Kwashinan ya bukaci mazauna jihar su tuntubi wannan lambobin don kai rahoto kan duk wani abu da ba su yarda da shi ba: 09034000060 and 08170189999.

Kara karanta wannan

Gwamna Masari: Gwamnati Da Hukumomin Tsaro Sun Gaza Tsare Yan Najeriya

Gwamna Masari: Gwamnati Da Hukumomin Tsaro Sun Gaza Tsare Yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Aminu Bello Masari, gwamnan Jihar Katsina, ya ce gwamnati ta gaza samarwa yan Najeriya tsaro, rahoton The Cable.

Masari ya bayyana hakan ne cikin wata hira da BBC Hausa ta yi shi da aka wallafa a ranar Talata 19 ga watan Yuli.

Ya ce mutane sun dogara ga gwamnati da jami'an tsaro ne domin su kare su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel