Yanzu-Yanzu: Hauhawar Farashi a Najeriya Ya Ƙara Tashi Wata Na Bakwai a Jere

Yanzu-Yanzu: Hauhawar Farashi a Najeriya Ya Ƙara Tashi Wata Na Bakwai a Jere

  • Farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙara hauhawa zuwa kaso 18.6% wata na Bakwai kenan a jere
  • Rahoton NBS ya nuna cewa an sami ƙarin kashi 0.7 fiye da hawan farashin na watan Mayun da ya shuɗe.
  • Kididdigar ta nuna cewa a ɓangaren kayan abinci hauhawar farashin ya ƙara ƙashi 20.6% inji rahoton NBS

Abuja - Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya sake tashi wata na Bakwai kenan a jere, inda a yanzu ya tashi zuwa kashi 18.6% a watan Yuni.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hakan na nufin an samu ƙarin kaso 0.7% idan aka kwatanta da 17.7% na watan Mayun da ya gabata.

Hauhawar farashin kayayyaki.
Yanzu-Yanzu: Hauhawar Farashi a Najeriya Ya Ƙara Tashi Wata Na Bakwai a Jere Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), ta bayyana haka a rahoton farashin kayayyaki (CPI) da ta fitar. Rahoton ya kuma bayyana cewa farashin kayan abinci ya karu da kaso 1.1% zuwa 20.6% daga 19.6% a watan Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Hukumar INEC ta faɗi ranar da zata rufe rijistar katin zaɓe bayan hukuncin Kotu

NBS ta bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A watan Yuni, 2022, hauhawar farashi ya ƙaru zuwa kaso 18.16% na shekara zuwa shekara. Wannan ya ɗarar wa wanda aka samu a bara da kaso 0.84 idan aka kwatanta da na watan Yuni, 2021 watau kaso 17.75."
"Dangane da na wata-wata kuma hawan farashin ya hau zuwa kashi 1.82% a watan Yuni, 2022, ya ƙaru na 0.003%da wanda kididdiga ta nuna a watan Mayu, (1.78%)."

Farashin kayan abinci ya tashi

Game da farashin abinci kuma, Leadership ta ruwaito NBS ta ce:

"Farashin jerin abinci ya tashi zuwa ƙaso 20.60%a watan Yuni, 2022 a kididdigar shekara zuwa shekara; ɗan sauyin da aka samu shi ne farashin ya sauka da kashi 1.23% idan aka kwatanta da 20.83% na watan Yuni, 2021."
"Canjin da aka samu a farashin abinci duba da irin wannan lokacin a shekarar data gabata ya yi sama sakamakon Annobar Korona da aka yi fama da ita."

Kara karanta wannan

Kaduna: El-Rufa'i' Ya Bada Umurnin A Ɗauki Sabbin Malamai 10,000 Bayan Ya Kori 2,000

A wani labarin kuma Hukumar zaɓe INEC ta ƙara wa'adin yin katin zaɓe zuwa 31 ga watan Yuli, 2022

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ƙarin lokacin cigaba da yin rijistar masu kaɗa kuri'a (CVR) zai ƙare ranar 31 ga watan Yuli, 2022.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da babbar Kotun tarayya ta yanke ranar Laraba. wanda ta yi watsi da ƙarar kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) wacce ta nemi a ƙara wa'adin ya zarce 30 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262