Harin gidan yarin Kuje: Dole ne a sauya fasalin tsaron Najeriya – Falana

Harin gidan yarin Kuje: Dole ne a sauya fasalin tsaron Najeriya – Falana

  • Femi Falana ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta sake duba tsarin tsaron Najeriya bayan harin da yan bindiga suka kai gidan yarin Kuje
  • Falana ya ce harin gidan yarin Kuje na matukar tayar da hankali saboda kasancewar sa daya daga cikin gidajen da aka fi tsarewa
  • Bayan Allah wadai da gwamnati Najeriya keyi babu wani mataki da take dauka wajen shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja : Wani dan kare hakkin bil’adama, Femi Falana, ya yi kira da a sake duba tsarin tsaron Najeriya bayan harin da yan bindiga suka kaiwa gidan yari Kuje dake birnin Abuja. Rahoton DailyTrust

Falana, Babban Lauyan Najeriya (SAN), ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya gana da gidan talabijin na Channels Tv cikin shirin Sunrise Daily a safiyar Laraba, ya ce babu wanda ya tsira a kasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hadimin Sheikh Ahmad Gumi ya fallasa sunan waɗan da suka kai kazamin hari gidan Yarin Kuje

Dan gwagwarmayar yana maida martani ne kan harin da 'yan ta'adda sama da 300 suka kai wa gida yarin inda suka yi amfani da muggan makamai da kuma bama-bamai don murkushe jami'an tsaro tare da sako da fursunoni a daren ranar Talata.

Falana
Harin gidan yarin Kuje: Dole ne a sauya fasalain tsaron Najeriya – Falana : FOTO VANGURAD
Asali: UGC
Falana ya ce, “Al’amari ne mai matukar tayar da hankali. Saboda gidan yarin Kuje kusan shine gidan kaso mafi tsaro a kasar..

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Don haka, idan ‘yan ta’adda za su iya kai hari cikin nasara tare da sakin fursunoni, lamarin ya bukaci a sake duba tsarin tsaro a kasar baki daya.
"Irin wannan hare-haren sun nuna a fili cewa akwai manyan matsaloli da gwamnati ta ki magance su dangane da tsaron kasar."
"Bayan Allah wadai da gwamnati ke yi babu wani mataki da take dauka akan matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta,"inji shi.

Kara karanta wannan

Harin gidan yarin Kuje: Atiku ya yi martani, ya bayyana babban damuwarsa kan lamarin

Babu wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a cocin Anambra – ‘Yan sanda

A wani labarin, Jihar Anambra - Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta karyata rahoton da aka wallafa a Facebook cewa wasu Fulani hudu sun kutsa cikin cocin Awada Grace na God a ranar Lahadi da nufin tayar da bam a cocin kamar yada jaridar Daily Trust ta rawaito.

Hukumar yansanda a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya ta bakin kakakinta, DSP Ikenga Tochukwu, ta ce labarin kanzon kuregen da aka wallafa Facebook, an yi shine domin a haifar da tashin hankali da kiyayyar kabilanci da na addini a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel