Zamfara: CDS Irabor ya Kalubalanci Umarnin Gwamna ga 'Yan Jihar na Mallakar Makamai

Zamfara: CDS Irabor ya Kalubalanci Umarnin Gwamna ga 'Yan Jihar na Mallakar Makamai

  • Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor ya kalubanci maganar da gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, na ba mutanen jihar damar mallakar bindigogi don kare kawunansu
  • A cewar Irabor, kiran bai kyautu ba saboda akwai jami'an tsaro da sauran hukumomin tsaro da ke kula da kalubalen tsaron da ya addabi jihar
  • Sai dai, ya cigaba da bayyana yadda Antoni-janar na tarayya ke da alhakin duba kundun tsarin dokoki don ganin idan gwamna na da wannan ikon

FCT, Abuja - Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, a ranar Litinin, ya kalubanci kira da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi ga mutanen jihar da su mallaki bindigogi don kare kawunansu daga farmakin 'yan bindiga.

Vanguard ta ruwaito cewa, Irabor ya ce kiran bai dace ba, saboda akwai jami'an tsaro da sauran hukumomin tsaro a wajen don magance matsalar.

CDS din ya zanta da manema labarai kan lamarin a wani taron hadin guiwar da Kwalejin Tsaro da Kwalejin Yaki na dakarun sojin Najeriya mai taken "Exercise Grand Nationale," a Abuja.

"Nayi imani, a nawa ra'ayin hakan ba abu bane mai bullewa.
"Tabbas, akwai matakan da mambobin hukumomin tsaro da rundunar soji, musamman 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro ke yi don magance matsalar rashin tsaro a Zamfara da kewaye.
"Baya ga haka, tabbas akwai matsaloli da sauran matsalolin da ya kamata ta shawo kai tare da amfani da dokokin da ke hannunsa don tabbatar da zaman lafiya da tsaro," cewar Irabor.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, Antoni-janar na tarayya ke da alhakin duba kundun tsarin dokokin don ganin idan gwamnan na da wannan ikon.

"Muna wurin ne saboda mun zo don kare hukumomin farar hula, wato 'yan sanda.

"Ba ma bukatar sake maimaita maganar lamarin da ya janyo tura sojoji fadin kasar, amma kamar yadda na fadi, mun yi iyakar kokarinmu wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a kowanne yankin kasar," a cewar.

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum

A wani labari na daban, 'yan bindiga a ranar Alhamis sun kone ofishin 'yan sanda, shaguna da gidaje uku a kauyen Zugu dake karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Sai dai, wani shugaban matasa a Bukkuyum, Abubakar Garba, yace babu wanda aka kashe a farmakin, Premium Times ta ruwaito.

Yace bayan harin, mazauna yankin da yawa sun yi gudun hijira zuwa Bukkuyum da sauran kauyukan dake karamar hukumar Gummi ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel