Yanzu-Yanzu: Ba a gama da ASUU ba, ma'aikatan NAFDAC sun tsunduma yajin aiki

Yanzu-Yanzu: Ba a gama da ASUU ba, ma'aikatan NAFDAC sun tsunduma yajin aiki

  • Kungiyar ma'aikatan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa sun tsunduma yajin aiki
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke kai ruwa rana da kungiyar malaman jami'a ASUU
  • Ya zuwa yanzu dai an samu rabuwar kai a kungiyar, ganin wasu yankunan kasar ba su amince a shiga yajin ba

Abuja - Kungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya (MHWUN) na hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta shiga yajin aikin, The Cable ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Laraba a hedikwatar hukumar ta NAFDAC da ke Abuja, shugaban kungiyar Auwalu Yusuf Kiyawa, ya ce yajin aikin ya fara ne daga lokacin da yake magana.

Ma'aikatan NAFDAC sun shiga yajin aiki
Yanzu-Yanzu: Ma’aikatan NAFDAC sun shiga yajin aikin bisa rashin biyansu alawus | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kiyawa ya ce kungiyar ba za ta janye yajin aikin ba har sai an biya alawus din ma’aikata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Nan Babu Dadewa Daliban Jami'o'i Zasu Koma Aji, FG

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa, yankin Legas da kudancin kungiyar ne kawai suka fara yajin aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce duk da cewa kungiyar baki daya ta amince a kan batun jin dadin ma'aikata, kungiyar ta Abuja da Arewacin Najeriya ba su amince da yajin aikin ba a matsayin mafita domin suna ganin bai dace ba.

Sahara Reporters ta rahoto cewa:

"A cewar daraktan gudanarwa, ma'aikatan sun ayyana yajin aikin amma kungiyar ta samu rabuwar kai.
“Mutanen Legas/kudu ne suke yajin aiki a halin yanzu. Abuja da yankin Arewa ba su shiga yajin aikin ba. Ba a taru a wuri daya ba. Shugaban yana Legas mataimakin shugaban kuma yana Abuja."

ASUU: Dalibai Sun Koka Kan Yajin Aikin Da Ya Ki Karewa, Sun Aike Sako ga FG

A wani labarin, yajin aikin malamai masu koyarwa na jami'o'i ya ki ci balle cinyewa yayin da ya cika watanni hudu cif tun bayan fara shi a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

Kara karanta wannan

AbdulMumini Jibrin ya daura hoton Kwankwaso ya 'badda kama, tambar Obama

Har a halin yanzu, babu wata takamaiman magana ko wani yunkurin janye yajin aikin da kungiyar ke yi sakamakon nuna halin ko in kula da gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna musu.

Legit.ng ta samu jin ta bakin wasu daliban jami'o'i kan yadda yajin aikin ya tsayar musu da karatunsa da kuma rawar da ya taka mai kyau ko akasin hakan a rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel