Yaron tsohon Gwamna ya jagoranci zanga-zangar da aka shirya saboda rashin tsaro

Yaron tsohon Gwamna ya jagoranci zanga-zangar da aka shirya saboda rashin tsaro

  • Tokunbo Ajasin ya jagoranci zanga-zangar da mutane suka shirya a farkon makon nan a Ibadan
  • Wannan matashi yana cikin ‘ya ‘yan tsohon gwamnan jihar Ondo, Marigayi PA Adekunle Ajasin
  • Ajasin yake cewa akwai bukatar Yarbawa su tashi domin su kare kansu daga harin ‘yan ta’adda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Tokunbo Ajasin wanda yana daya daga cikin ‘ya ‘yan Marigayi Cif Adekunle Ajasin ya shiga zanga-zangar da aka shirya a ranar Litinin din da ta wuce.

Daily Trust ta kawo rahoto an ga Tokunbo Ajasin wajen zanga-zangar da matasa da dattawa mazauna garin Ibadan, jihar Oyo suka yi a farkon makon nan.

Micheal Adekunle Ajasin ya yi gwamna a tsohuwar jihar Ondo na shekaru hudu a jam’iyyar UPN. 'Dan siyasar ya rasu ne tun a shekarar 1997 yana shekara 88.

Kara karanta wannan

Akwai ƙura: Ibo sun buɗa wuta, sun ce bai dace Atiku ya dauki Wike a Jam’iyyar PDP ba

Watakila Ajasin yana cikin daula, amma wannan bai hana shi fita kan titi domin jawo hankalin hukuma da mutane a kan irin abubuwan da su ke faruwa ba.

Masu zanga-zangar sun bukaci kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a kudu maso yamma.

Tokunbo Ajasin ya jagoranci jama’a a wannan zanga-zangar lumanar da aka shirya a garin Ibadan, su na dauke da rubutu da za su ankarar da gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnoni
Gwamnonin Kudu maso yamma Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Baya ga haka, wasu masu zanga-zangar sun cika titunan babban birnin jihar Oyo na Ibadan, su na masu yin kira ga al’umma da su shirya kare kansu da kansu.

Dalilin yin zanga-zangar shi ne ganin hallaka mutane da ake yi babu gaira babu dalili da garkuwa da mutane da fyaden da ake fama da shi a jihohin Yarbawa.

Ba yau aka fara ba

Kara karanta wannan

Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

Masu zanga-zangar sun ce kashe Bayin Allah da aka yi a cocin St Francis Catholic Church da ke garin Owo a jihar Ondo ba shi ne farko da aka yi a yankin ba.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, masu zanga-zangar sun yi ikirarin ‘ya ta’adda sun taba kai irin wannan mugun hari a Igangan a garin Ibarapa da ke jihar Oyo.

A rahoto daga Punch, an ji Steve Abioye mai kare hakkin Yarbawa yana irin wannan kira. Alabi Arogunmasa mai shekara 75 ya nemi matasa su tashi tsaye.

Gwamnatin El-Rufai

Dazu an ji cewa Malam Nasir El-Rufai ya yi abin da ba a taba gani ba a tarihin Kaduna, ya nada mace a matsayin kwamishinan kananan hukumomi na jihar.

Watakila a Najeriya babu jihar da maza ba su fi mata yawa a majalisar zartarwa ba, amma a jihar Kaduna, mata tara ne kwamishononi, maza kuma su takwas.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikici ya barke yayin da aka kashe wani jigon jam'iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel