Mai saida askirim, dillalin tumatir: Shettima ya nemi gafarar Osinbajo da Lawan kan cin zarafinsu da yayi

Mai saida askirim, dillalin tumatir: Shettima ya nemi gafarar Osinbajo da Lawan kan cin zarafinsu da yayi

  • Daraktan kamfen na Tinubu, Kashim Shettima ya bai wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan hakuri game da furucin da ya yi a kansu
  • Shettima yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma'a, ya ce Osinbajo mutum ne mai fara'a kuma mutane masu fara'a sun cancanci tallar askirim da siyar da gugguru
  • Haka zalika ya nuna shakkunsa game da Ahmad Lawan a kan iya gudanar da mulkin yadda ya dace, hakan ya sa jama'a da dama suka yi amfani da haka wajen zolayar 'yan takarar

Babban daraktan kungiyar kamfen na Tinubu, Kashim Shettima ya ba wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan hakuri game da furucin da ya yi yayin wata tattaunawa da manema labarai.

A ranar Juma'a, yayin zantawa da Channels TV, Shettima ya ce mataimakin shugaban kasa ' mutum ne mai fara'a kuma mutane masu fara'a sun cancanci su dinga tallan askirim da gugguru.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Da duminsa: Bam ya tashi, 'yan bindiga sun bude wa masu bauta wuta a cocin Ondo
Da duminsa: Bam ya tashi, 'yan bindiga sun bude wa masu bauta wuta a cocin Ondo. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Haka zalika, ya yi tantama game da iya gudanar da mulki da ficen Lawan.

A wata takarda da ta fita ranar Lahadi, Shettima ya ba su biyun hakuri, inda ya ce ya yi wannan furucin ne don ganin 'ya cika wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu alkawarin da ya daukar mai na kare masa mutuncinsa ga wadanda ba su riga sun tsaida ra'ayi a kan wanda za su zaba a zaben fidda gwanin APC da ke karatowa, Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ban taba burin cin mutuncin wani 'dan takara ba, kuma ba zan taba yin haka ga abokanai na na hakika ba. Cikinsu babu abokin hamayya, saboda haka takarar ba barazana bace gare mu. Sun bayyana ne ta wannan sigar don su zama masu da tutar jam'iyyar a zaben 2023, amma su din aminanmu ne a wannan gasar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

"Furucin da nayi a kan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ba don cin zarafinsu bane. Ban taba burin yi musu ba a baya amma, sai dai don kokarin kare mutuncin da kimar 'dan takarar da nake karewa, amma abun da ya fi komai mahimmanci shi ne mu ga APC ta yi nasara a zaben shugaban kasar shekarar 2023.
"Ban yi furucin don nuna su din ba su cancanci takara ba, sai don in nuna cewa su din ba abokan takarar da za su zamo barazana bane. Saboda haka, na amince da laifin furuci na kuma zan so magoya bayanmu da kada su dauki kalamai na da wata manufa kuma kada su fassarasu a wata hanyar cin zarafi ga abokaina kuma masoya na."

Dukkan biyun Osinbajo da Lawan abokan takarar tsohon gwamnan Legas din ne, Bola Tinubu da wasu 'yan takarar daban.

APC za ta gabatar da zaben fidda gwanin jam'iyyar gobe don fidda zakaran gwajin dafi daga cikin 'yan takararta 23.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya

Babu 'dan takarar da APC ta yi watsi da shi yayin tantancewa, Mamban Kwamitin Tantancewa

A wani labari na daban, wani mamban kwamitin tantancewa na jam'iyyar APC ya yi karin haske dangane da batun jam'iyyar na dakatar da wasu 'yan takarar shugaban kasa cikin mutane 23 da suka bayyana gabanta.

Ya bayyana wa Premium Times a daren Juma'a cewa, ba daidai ba ne rahoton da aka dinga yadawa dangane da cewa kwamitin ta dakatar da 'yan takara 13.

Mamban wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce duk jerin 'yan takarar shugabancin kasar da suka gabatar da kawunansu gaban kwamitin sun cancanci tsayawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel