Da duminsa: Bala Mohammed ya lashe zaben fidda gwanin PDP a jihar Bauchi

Da duminsa: Bala Mohammed ya lashe zaben fidda gwanin PDP a jihar Bauchi

  • Kamar yadda akayi tsammani, Gwamnan Bauchi ya lashe sabon zaben fidda gwanin PDP a jihar
  • A ranar Asabar jam'iyyar PDP a jihar ta gudanar da sabon zabe bayan janyewan Mohammed Ibrahim Kashim
  • A ranar Juma'a, Gwamnan jihar Bauchi ya sake nada Ibrahim Kashim matsayin Sakataren gwamnatin jihar

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Bala ya lashe zaben ne a sabon zaben da ya gudana biyo bayan janyewar wanda ya lashe zaben na farko, Ibrahim Kashim.

A zaben da ya gudana yau Asabar, 4 ga watan Yuni, Bala Mohammed kadai ne dan takara kuma shi kadai dukkan deleget na kananan hukumomi 20 suka kadawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dandazon jama'a tarbi Tambuwal a Sokoto bayan zaben fidda gwanin PDP

A jawabinsa, ya mika godiyarsa ga Ibrahim Kashim, wanda ya janye masa don yayi takara.

Bala Mohammed
Da duminsa: Bala Mohammed ya lashe zaben fidda gwanin PDP a jihar Bauchi Hoto: Kauran Bauchi Media TV
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan janyewa Gwamnan Bauchi, an mayar da shi kujerarsa ta Sakataren Gwamnati

Bayan janyewa daga takarar kujerar Gwamnan jihar Bauchi, an mayar da Ibrahim Kashim kujerarsa ta Sakataren gwamnatin jihar Bauchi.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, a jawabin da ya fitar ranar Alhamis a garin Bauchi.

Ya bayyana cewa Gwamna Bala Muhammad ya mayar da Kashim kujerarsa ne saboda mutum ne mai gaskiya kuma mai kwarewan gaske.

Asali: Legit.ng

Online view pixel