Duniya kenan: An kama wasu mutane da suka hallaka yaro dan shekara 4 da sunan tsafi

Duniya kenan: An kama wasu mutane da suka hallaka yaro dan shekara 4 da sunan tsafi

  • Rundunar yan sanda a jihar Neja sun damke wasu mutane biyu da ake zargi da kashe yaro dan shekara hudu
  • Wadanda ake zargin sun cire wasu sassa na yaron domin yin tsafi da shi a karamar hukumar Lapai ta jihar
  • Tuni fusatattun matasa a yankin suka kona gidaje da shagudan mutumin da aikata hakan mai suna Emmanuel wanda ke siyar da kayan gini

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - Rundunar yan sandan Lapai sun ceci wasu mutane biyu daga hannun fusatattun matasa bayan an same su da gawar wani yaro dan shekara hudu da ya bata tsawon kwanaki hudu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a garin Lapai da ke karamar hukumar Lapai ta jihar Neja.

An tattaro cewa wanda ake zargin mai suna Emmanuel wanda ke siyar da kayan gini ya hada kai da mai gadinsa wajen sace yaron da kuma kashe shi.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Ƴan Sanda Sun Tabbatar An Ƙona Gidaje 6 Da Shaguna 7 a Bauchi

Duniya kenan: An kama wasu mutane da suka hallaka yaro da shekara 4 da sunan tsafi
Duniya kenan: An kama wasu mutane da suka hallaka yaro da shekara 4 da sunan tsafi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Majiyoyi a Lapai sun bayyana cewa masu laifin sun kashe yaron sannan suka cire sassan jikinsa da suka hada da gaban shi, idanuwa, kunnuwa da zuciyarsa sannan suka saka gawarsa a cikin buhu don mai gadin ya je ya jefar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai gadin ya dauki hayar babur zuwa wajen wani kogi da nufin jefar da gawar amma sai dan achabar ya lura da jinin da ke zuba daga buhun sannan ya je ofishin yan sandan don kai rahoto.

Yan sanda sun shirya sannan suka tafi kogin, inda suka kama mai gadin.

An tattaro cewa ya fallasa cewar maigidansa ne ya aike shi ya jefar da gawar sannan cewa sune suka sace yaron da ya bata yan kwanaki da suka gabata.

Yan sandan sun kuma je gidan Emmanuel don kama shi inda suka tarar da fusatattun matasa sun taru suna farfasa gidan, yayin da suke shirin rufe shi da duka.

Kara karanta wannan

Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi duk rana a hayar jirgi

An tattaro cewa shiga lamarin da yan sanda suka yi ya fusata matasan inda suka kona gidan da shagonsa.

Wani mazaunin yankin, Mahmood Abdul, ya bayyana cewa basu taba sanin cewa Emmanuel dan tsafi bane, kuma cewa ya yi sa’a basu kama shi ba kafin yan sanda su zo.

“Akwai miyagun mutane a koina, Emmanuel na daya daga cikinsu. Mun kona gidansa. Mun so ace shi muka samu da mun kashe shi.”

Legit Hausa ta tuntubi Wani mazaunin Lapai mai suna Mallam Daddy Usman inda ya bayyana cewa sun kadu matuka da faruwar lamarin.

Ya ce:

“Kai abun ya girgizamu sosai. Mun dai san mutumin yana da kudi don yana sana'ar siyar da kayan gine-gine ne, amma bamu taba sanin kudin jini yake yi ba. Idan ka ga gidansa a unguwar babu irin sa. Sannan ya budewa matarsa katafaren wajen siyar da kaya, idan dai kaya masu kyau kake so toh duk Lapai a shagonsu ne za ka samu.

Kara karanta wannan

Adamawa: 'Yan sanda sun budewa masu garkuwa da mutane wuta, sun halaka 3

“Yanzu haka duk an kona gidajen da shagunansa, harda gidan da yake bayar da haya mai dauke da dakuna kusan 15. Yanzu dai an dauke shi zuwa ofishin CID a Minna. Mun ji wai ya ce ba shi kadai bane amma dai bai bayyana sunayen sauran mutanen ba. Allah dai ya tsare mu.”

Kakakin yan sandan jihar, DSP Abiodun Wasiu, ya tabbatar da lamarin da kamun sannan ya bayyana cewa an fara bincike kan lamari, rahoton The Cable.

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Fille Kan Ɗan Majalisar Najeriya Kwanaki Bayan Sace Shi

A wani labari na daban, 'Yan bindiga sun halaka dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguta II a Jihar Anambra, Dr Okechukwu Okoye wanda aka fi sani da 'Okey Di Okay', rahoton The Cable.

An sace Okoye ne, dan asalin garin Isuofia, garinsu Chukwuma Soludo, gwamnan Anambra a Aguata a ranar Lahadi 15 ga watan Mayu tare da Cyril Chiegboka, direktan kamfen dinsa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Ku san 'yan takara 5 na shugaban kasa a APC da ba za su da ginshikin siyasa

Da ya ke tabbatar wa The Cable rasuwar, Tochukwu Ikenga, kakakin yan sandan Jihar Anambra, ya ce an tsinci gangan jikin dan majalisar a Nnobi a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng