Adamawa: 'Yan sanda sun budewa masu garkuwa da mutane wuta, sun halaka 3
- 'Yan sandan jihar Adamawa sun sheke uku daga cikin wadanda ake zargin 'yan bindiga ne, gami da yin ram da wasu biyu daga bisani suka ceto wani da aka yi garkuwa da shi
- Kakakin rundunar ne ya sanar da yadda a ranar 17 ga watan Mayu tawagar 'yan sanda da mafarautan karamar hukumar Fufore suka kai samame ga wasu hatsabiba a tsaunin Samlo
- Luguden wutar da mafarautan da 'yan sanda suka wa hatsabiban ne ya tilasta wasu daga cikinsu tserewa da raunukan harsasai bayan sun sheke uku gami da damke biyu daga ciki
Adamawa - Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta bayyana yadda jami'an ta suka halaka wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne guda uku, gami da cafke wasu biyu, sannan suka tseratar da wani da aka yi garkuwa da shi guda daya yayin da suka kai samame tare da mafarauta a karamar hukumar Fufore dake jihar.
Suleiman Nguroji, kakakin rundunar ne ya sanar da hakan wata takarda da ya fitar ranar Alhamis a Yola, Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana yadda lamarin ya auku a ranar 17 ga watan Mayu, a tsaunin Sambo, wanda ke tsakanin yankin Chigari da anguwan Gurin.
"An yi nasara a samamen da jami'an rundunar 'yan sandan marabar Gurin da manoman tsaunin Sambo, wanda ke tsakanin Chigari da dagacin Gurin cikin karamar hukumar Fufore suka kai.
"Sakamakon wadannan nasarorin ya biyo bayan matakan da rundunar ta tsara don duba lamurran garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, munanan ayyukan 'yan bindiga, da dai sauran laifuka.
"Wandanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin da su ka yi ido biyu da jami'anmu sun yi musayar wuta da su, a sanadin haka ne, suka sheke uku daga cikin su, tare da damko biyu," ya bayyana.
Rikicin yan achaba da yan kasuwa: Ministan Abuja ya yi umurnin rufe kasuwar Dei-Dei har sai baba-ta-gani
A cewarsa, samamen yayi nasarar ceto wani da aka yi garkuwa da shi, Buba Hamidu, mazaunin kauyen Samlo cikin karamar hukumar Fufore.
Wasu daga cikin hatsabiban sun tsare tare da raunukan harsasai, a cewar kakakin.
Ya kara da bayyana yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa, Sikiru Akande, ya jinjinawa DPO marabar Gurin, wanda ke kula da lamurran Chigari da kokarin da mafarautan su ka yi.
Kwamishinan 'yan sandan ya tabbatar wa gwamnati da mazauna jihar da tabbatar da bankado mabuyar hatsabiba da wuraren ta'addancinsu a fadin jihar.
"Shugaban 'yan sandan ya umarci tawagar OC da su cigaba da bincike, sannan a tabbatar an gurfanar da wadanda ake zargin," a cewarsa.
Katsina: Ƴan sanda sun sheƙe 'yan bindiga 6, sun kwace makamai da dabbobin sata
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce ta dakile harin 'yan bindiga a kauyen Dabaibayawa na Batagarawa da kauyen Dankiri na karamar hukumar Dutsinma.
Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Katsina akan ayyukansu na cikin kwanakin nan a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng