Shirin 2023: 'Yan takara 5 na shugaban kasa a APC da ba za su da ginshikin siyasa

Shirin 2023: 'Yan takara 5 na shugaban kasa a APC da ba za su da ginshikin siyasa

  • Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, a hankali ana bambance aya da tsakuwa
  • Guguwar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyya mai mulki ba shi ne tabbacin samun nasara ba kasancewar siyasa ta kasance wasa ce da ba ta tabbas
  • A yayin da ake samun wasu ‘yan takarar da ke rike da madafun ikonsu kuma ke sa wa a rai za su gaji Buhari, wasu har a ransu sun san ba za su kai labari ba, neman suna ne kawai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Kamar yadda yake faruwa a kowane yanayi na siyasa a Najeriya a duk lokacin da ake gudanar da zabuka, a kullum sai an samu masu fafutukar takara da masu neman suna.

Irin wannan al’amari a halin yanzu yana kara jan hankali a jam’iyyar APC mai mulki a daidai lokacin da ake tunkarar zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

'Yan takarar APC da ba lallai su kai labari ba a zaben 2023
Shirin 2023: 'Yan takara 5 na shugaban kasa a APC da ba za su kai labari ba | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Duk da yake akwai wadanda suke da sha'awar takara kana suke da ginshikin siyasa na gaske kuma suke ta kokarin ganin sun gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, wasu kuwa suna nan ne a matsayin cikon lamba a jerin 'yan takara.

Kamar dai yadda aka sani, Legit.ng bata yi kasa a gwiwa ba wajen tattaro muku wadannan 'yan takara. Ga su kamar haka:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin 'yan takarar da sun san ba za su kai labari ba

1. Barr. (Mrs) Uju Kennedy Ohnenye

Ita ce mace daya tilo a cikin tseren takarar shugaban kasa kuma a fili bata saka takarar a rai ba.

Ohanenye ta ce adadin mazan da ke neman tsayawa takara ba zai razana ta ba, amma ba ta yi wani yunkuri na jan hankalin 'delegates' ko tuntubarsu a jihohin tarayya daban-daban ba, wanda halan barazana ce ta siyasarta.

Kara karanta wannan

2023: Ƴan Takara 3,000 Ne Za Su Fafata Don Neman Tikitin Takarar Majalisun Jihohi a APC

2. Fasto Nicholas Felix Nwagbo

Shi Fasto ne dan Najeriya da ke zaune a Amurka wanda ke shugabantar Miracle Church International.

Fasto Nwagbo ya ce yana da hedikwatar cocinsa a New York, mai rassa a New Jersey, Texas Atlanta, da Najeriya. Babu wani abu da aka sani game da shi a fagen siyasa. Lamarin dai ba boyayye bane, kawai yana bata lokacinsa ne.

3. Chief Ikeobasi Mokelu

Cif Mokelu ya kasance ministan yada labarai da al'adu a zamanin gwamnatin marigayi tsohon shugaban Najeriya Janar Sani Abacha.

An ce yana da kusanci da Shugaba Buhari, amma duk da haka, ba shi da wani ginshiki na siyasa a APC. Ba kasafai ake ganinsa a bainar jama'a ba, kuma dai hakan a bayyane yake barazana ce ga takararsa.

4. Tein Jack-Rich

Jack-Rich shi ne Shugaba kuma wanda ya kafa kamfanin Belemaoil Producing Limited, kamfanin hako da habaka man fetur na farko a Najeriya.

Kara karanta wannan

Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu

Ya fito karara ya taka rawar gani a harkar man fetur da iskar gas amma da alama bai fahimci cewa siyasa da rigimar kasuwanci duniyoyi ne biyu da suka yi hannun riga ba.

5. Pastor Tunde Bakare

Limamin coci mai shekaru 67 da haihuwa. Ya kasance abokin takarar shugaba Buhari a zaben shugaban kasar Najeriya na 2011 karkashin rusasshiyar jam'iyyar CPC ta wancan lokacin.

Baya ga hayaniya da ake ta yadawa a kafafen yada labarai, ba a san Bakare a matsyain jigon dan jam’iyyar APC ne mai karfi ba.

Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu

A wani labarin, jigon jam'iyyar All Progressives Congress APC kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa mutum mai hikima da kwazo ake bukata matsayin shugaba ba lebura ko maji karfi ba.

A kalamansa, aikin shugaban kasa ba na hawa kan tsauni bane ko diban kankare, aikinsa tunani da amfani da kwakwalwarsa.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu: Majiya ta ce APC ta gama zaban wanda zai gaji Buhari a 2023

Yace: "Ba dan damben WWE ake bukata ba, mai tunani kan yadda za'a samar da tsaro, wanda zai yi nazari kan lamuran tattalin arziki kuma ya inganta ake bukata."

Asali: Legit.ng

Online view pixel