Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi a duk rana a hayar jirgi

Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi a duk rana a hayar jirgi

  • Gwamnonin jihohi 9 ne suke batar da miliyoyin kudi domin daukar hayar jiragen sama su na kamfe
  • Wadannan gwamnoni su na amfani da jirage zuwa yawon yakin neman zaben shugaban kasa da suke yi
  • Masu takarar shugaban kasa cikin gwamnoni masu-ci sun hada da: Wike, Fayemi, da Tambuwal

Daily Trust ta fitar da wani rahoto na musamman a ranar Juma’a, 20 ga watan Mayu 2022 da ya nuna yadda kudi su ke tafiya wajen hayar jiragen sama.

Mutane 38 su ke neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyun PDP da APC mai mulki. Daga cikin masu harin tikiti akwai wasu Gwamnoni jihohi tara.

Binciken da jaridar tayi ya nuna abubuwa sun tsaya cak a wadannan jihohi. Ana zargin hakan bai rasa nasaba da yadda ake kashe kudin al’umma a kamfe.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Ku san 'yan takara 5 na shugaban kasa a APC da ba za su da ginshikin siyasa

Nawa ake hayar jirgin sama?

Idan mutum zai dauki hayar jirgin sama na tsawon sa’a daya, zai kashe tsakanin $7000 da $10000. Farashin ya danganta ne da irin girman jirgin da aka dauka.

A yadda ake canjin Dalar Amurka yanzu a kasuwar canji a kan kusan N600, mutum zai kashe tsakanin Naira miliyan 4.2 zuwa Naira miliyan 6 a duk awa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani wanda yake da ido a harkar ya ce farashin zai iya fin haka idan aka dauki jirgi irinsu Challenger ko Beechcraft Hawker mai daukar fasinja fiye da 10.

Akwai manyan jirage kamar Embraer ERJ 145 da za su iya cin mutum 50. Sannan kudin da za a biya ya danganta da dadewar da za ayi a filin sauka da tashi.

Gwamnan Ribas
Nyesom Wike a Kaduna Hoto: @Topboychriss Daga: Twitter
Asali: Twitter

Kasuwa ta budewa masu jirgi

Kamar yadda wani mai jirgin sama ya shaidawa jaridar, kasuwarsu ta bude tun da aka fara yawon yakin neman takarar zama shugaban kasan 2023.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin jihohi 17 da za su sauka daga kan kujerar mulki nan da watanni 12

Ibrahim Aliyu masanin harkar tsaro ne, wanda ya bayyana cewa ana yawan amfani da jirage ne saboda gwamnonin ba za su iya yawo da motoci a titi ba.

A halin yanzu ana fama da matsalar tsaro a jihohi barkatai, wannan ta sa gwamnonin da ke harin kujerar shugaban kasa ke batar da dukiya a hayar jiragen.

Yadda gwamnonin ke yawo

Nyesom Wike ya ziyarci jihohi 20 zuwa yanzu, watakila yana yawo ne a jirgin gwamnatin Ribas, ko ya yi haya a kasuwa, duk dai wadaka da kudin kasa ne.

Shi ma Gwamnan Sokoto ya je Taraba, Borno, Yobe, Kogi, Niger, Gombe, Kaduna, Zamfara, Ribas, Delta, Imo, Kebbi, Kogi, Bayelsa, Nasarawa, Osun da Ogun.

Jaridar ta ce Gwamna Kayode Fayemi ya ziyarci jihohi 16, an ga Bala Mohammed a jihohi 12. Gwamna Udom Emmanuel ya yi amfani da jirgi ya je jihohi shida.

Gwamnoni 9 za su nemi tikiti

Kara karanta wannan

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

Ku na da labari cewa a cikin gwamnoni,n da ke takara Bala Mohammed ne yake kan wa’adinsa na farko. PDP ta na da gwamnoni hudu, sai APC na da biyar.

Sauran Gwamnonin su ne; Nyesom Wike, Kayode Fayemi, Aminu Tambuwal, Emmanuel Udom, Ben Ayade, David Umahi, Badaru Abubakar da Yahaya Bello.

Asali: Legit.ng

Online view pixel