Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Fille Kan Ɗan Majalisar Najeriya Kwanaki Bayan Sace Shi

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Fille Kan Ɗan Majalisar Najeriya Kwanaki Bayan Sace Shi

  • Wasu miyagun yan bindiga sun halaka Dr Okechukwu Okoye, dan majalisar jihar Anambra mai wakiltan mazabar Aguta II yan kwanaki bayan ace shi
  • An fara gano gangan jikinsa babu kai, sannan daga bisani aka gano kansa cikin wani kwalli a tashan Chisco a garin Amichi da rubutu a gefe
  • Rundunar yan sandan Jihar Anambra ta bakin kakakinta, Tochukwu Ikenga ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma bada tabbacin za kamo wadanda suka aikata laifin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Anambra - 'Yan bindiga sun halaka dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguta II a Jihar Anambra, Dr Okechukwu Okoye wanda aka fi sani da 'Okey Di Okay', rahoton The Cable.

An sace Okoye ne, dan asalin garin Isuofia, garinsu Chukwuma Soludo, gwamnan Anambra a Aguata a ranar Lahadi 15 ga watan Mayu tare da Cyril Chiegboka, direktan kamfen dinsa.

Kara karanta wannan

Shugaban kamfanin buga kudi ya ajiye aiki, ya shiga neman takara gadan-gadan a APC

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Fille Kan Ɗan Majalisar Najeriya Kwana Kaɗan Bayan Sace Shi
'Yan Bindiga Sun Fille Kan Ɗan Majalisar Najeriya Kwana Kaɗan Bayan Sace Shi a Anambra. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Sanda Sun Tabbatar Da Rasuwar Okoye

Da ya ke tabbatar wa The Cable rasuwar, Tochukwu Ikenga, kakakin yan sandan Jihar Anambra, ya ce an tsinci gangan jikin dan majalisar a Nnobi a ranar Asabar.

Ikenga ya kuma ce ana cigaba da bincike, ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar Echeng Echeng ya tabbatarwa iyalan dan majalisar cewa za a kamo wadanda suka aikata laifin.

An gano kan marigayin a tashar Chisco

A ruwayar The Punch, an gano kan marigayin dan majalisar a tashar Chisco a garin Amichi a jihar Anambra a ranar Asabar.

A wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, an hangi kan cikin wani kwali a gefen titi da rubutu a takarda a gefensa.

An yi kokarin ji ta bakin hadimin gwamna, Christian Aburime game da lamarin amma bai amsa kira ko sakon tes ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel