Zagin Annabi: Ƴan Sanda Sun Tabbatar An Ƙona Gidaje 6 Da Shaguna 7 a Bauchi

Zagin Annabi: Ƴan Sanda Sun Tabbatar An Ƙona Gidaje 6 Da Shaguna 7 a Bauchi

  • 'Yan sanda sun kai dauki karamar hukumar Warji da ke Jihar Bauchi musamman don kwantar da tarzomar da ta tashi saboda batancin da ake zargin wata ta yi wa Annabi
  • Wasu matasa sun bazama neman wata Rhoda Jatau bisa zarginta da batanci inda rashin ganinta ya sa su ka far ma duk wasu kiristoci da ke yankin
  • Ganau sun bayyana yadda aka yi asarar dukiyoyi yayin da mutane da dama su ka raunana wanda hakan ya sa kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’ansa yankin

Jihar Bauchi - Saboda wani rikici da ya balle a Jihar Bauchi akan zargin batancin da aka yi ga Annabi, ‘yan sanda sun je kwantar da tarzomar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Lamarin ya auku ne a karamar hukumar Warji da ke jihar yayin da wasu matasa su ka bazama neman Mrs Rhoda Jatau, matar da ake zargin ta yi batancin.

Bauchi: Yan sanda sun kai dauki yayin da rikici ya balle akan batanci
'Yan sanda sun kai dauki yayin da rikici ya balle akan batanci a Bauchi. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani ganau ya ce fusatattun matasan sun afka yankin Katanga, hedkwatar karamar hukumar Warji a ranar Juma’a su na neman Jatau.

An samu rahoto akan yadda wasu mazauna yankin su ka tsere da Jatau don nema mata hanyar tsira, wanda hakan ya janyo asarar dukiyoyi har da gidaje 11 da aka banka wa wuta bisa ruwayar Daily Trust.

Malaman addinin yankin sun sanar da manema labarai cewa su na ta iyakar kokarinsu wurin kwantar da hankalin matasan.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Umar Mamman Sanda, ya shaida yadda ya tura jami’ansa yankin kuma ya umarci a yi bincike akan lamarin.

Kara karanta wannan

Ana Zaman Ɗar-Ɗar Yayin Da Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai

Jami’an tsaro sun kwantar da tarzomar yankin

Yayin bayar da bayani akan yadda lamarin ya auku, jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Ahmed Wakil ya ce:

“A ranar 20 ga watan Mayun 2022, wasu matasa sun banka wa gidaje 6 da shaguna 7 wuta yayin da su ka ji wa mutane da dama raunuka saboda wani sako mai cike da batanci da wata Rhoda Jatau, mai shekaru 40, ma’aikaciyar lafiya a karamar hukumar Warji ta tura ta kafar sada zumunta.
“Tuni aka tura jami’an tsaro yankin don tabbatar da an kwantar da tarzomar. Yanzu komai ya dawo daidai amma jami’an tsaro su na ci gaba da sintiri a yankin don tabbatar da tsaro.”

‘Yan sanda sun bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa kuma ya bi doka domin jami’an tsaro ba za su gushe ba har sai sun tabbatar komai ya dawo daidai.

A makon da ya gabata aka halaka wata Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilimin Shehu Shagari bisa zarginta da batanci ga Annabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel