Zagin Annabi: Kungiyoyin CAN da JNI sun gargadi matasa a kan yin kalaman tunzura

Zagin Annabi: Kungiyoyin CAN da JNI sun gargadi matasa a kan yin kalaman tunzura

  • Kungiyar kiristocin Najeriya da na Jama’atu Nasril Islam (JNI) a jihar Kaduna, sun ja hankali hankalin matasa a kan yin kalaman tunzura a shafukan soshiyal midiya
  • A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar, kungiyoyin sun bukaci mabiyansu da su rungumi zaman lafiya tare da hakuri da juna
  • Hakan ya biyo bayan wani sako da wani matashi ya wallafa a dandalin sada zumunta yana mai kira ga mutanen Kudancin Kaduna da su dauki doka a hannunsu kan kisan Deborah

Kaduna - Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen karamar hukumar Jema’a da kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a jihar Kaduna, sun yi kira ga mutane musamman matasa, da su kula da zantukansu a shafukan soshiyal midiya da janyewa daga kalaman tunzura.

Sakataren JNI a Jema’a, Alhaji Ilyasu Musa, mataimakin sakataren CAN, Reverend Ido Yakubu, da shugaban karamar hukumar, Markus Yunana Barde, a wata sanarwa ta hadin gwiwa, sun yi kira ga shugabannin gargajiya da na addinai da su yi wa’azin zaman lafiya ga al'ummarsu don su rungumi zaman lafiya da hakuri da juna.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Zagin Annabi: Kungiyoyin CAN da JNI sun gargadi matasa a kan yin kalaman tunzura
Zagin Annabi: Kungiyoyin CAN da JNI sun gargadi matasa a kan yin kalaman tunzura Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

“Duk wanda aka kama yana tada tarzoma ko kuma yana gudanar da ayyukan da ka iya kawo cikas ga yanayi ko zaman lafiya to a kama shi kuma a yi maganinsa yadda ya kamata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mun yanke shawarar zama masu bin doka da zama cikin lafiya da juna duk da banbancin addini da kabila da kuma gargadin mutanenmu kan daukar doka a hannunsu.”

Sun fitar da jawabin ne bayan wani taron tsaro da aka yi a fadar sarkin Jema’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad, a Kafanchan, Daily Trust ta rahoo.

Idan dai za a iya tunawa, wani mai suna Isaac, wanda aka fi sani da Marafan Tsoriyang, a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta ya yi kira ga mutanen Kudancin Kaduna da su dauki doka a hannunsu.

Ya yi martani a shafinsa na Facebook sannan ya kuma yi sakon murya da ya yi fice kan kisan Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilimi na Shehu Shagari, Sokoto, wacce aka halaka kan zagin Annabi Muhammad.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kaduna ta haramta gudanar da zanga-zangar addini a jihar, inda tun a ranar Litinin din da ta gabata aka jibge tankokin yaki masu sulke a duk kofofin shiga birnin na Kafanchan.

Kisan Deborah: Ku mutunta koyarwar sauran addinai, CAN ta roki Kiristoci

A gefe guda, kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta roki kiristoci da su dunga mutunta koyarwar addinin sauran mutane, inda ta bayyana cewa akwai bukatar dukka cibiyoyin addini su dunga koyar da mabiyansu ilimin mutunta sauran addinai.

Shugaban kungiyar CAN, Dr Samson Ayokunle yayin da yake jawabi a shirin sassafe na Arise TV, a ranar Litinin, ya ce yakamata a koyar da dalibai yadda za su dunga kai kara ga hukumomin da suka dace ko hukumomin doka, Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng