Kisan Deborah: Ku mutunta koyarwar sauran addinai, CAN ta roki Kiristoci

Kisan Deborah: Ku mutunta koyarwar sauran addinai, CAN ta roki Kiristoci

  • Kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN ta roki mabiya addinin kirista da su dunga mutunta sauran addinai
  • CAN ta kuma bukaci dukka cibiyoyin addini da su dunga koyar da mabiyansu ilimin mutunta sauran addinai
  • Hakan ya biyo bayan kisan wata daliba mai suna Deborah Samuel da fusatattun matasa suka yi a jihar Sokoton kan zagin Annabi

Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta roki kiristoci da su dunga mutunta koyarwar addinin sauran mutane, inda ta bayyana cewa akwai bukatar dukka cibiyoyin addini su dunga koyar da mabiyansu ilimin mutunta sauran addinai.

Shugaban kungiyar CAN, Dr Samson Ayokunle yayin da yake jawabi a shirin sassafe na Arise TV, a ranar Litinin, ya ce yakamata a koyar da dalibai yadda za su dunga kai kara ga hukumomin da suka dace ko hukumomin doka, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Deborah Samuel: Ƴan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

Kisan Deborah: Ku mutunta koyarwar sauran addinai, CAN ta roki Kiristoci
Kisan Deborah: Ku mutunta koyarwar sauran addinai, CAN ta roki Kiristoci Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya ce:

“Akwai bukatar koyar da ilimin mutunta sauran addinai don mutum ya san abun da mutanen sauran addinai da ke kewaye da shi basa so da kuma mutunta su. Idan akwai wannan mutuntawar a kasar nan, za a samu zaman lafiya. Kada ka dauki hukunci a hannun ka idan wani ya yi maka laifi. Ka kai kara yadda ya dace. A yanzu kai ya waye. Ba a zamanin jahiliya muke ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A iya sanina, ban ga an ambaci sunan kowasu jiga-jigan addini a takardun da na samu daga mutanenmu ba a Sokoto, wadanda suke kiristoci.
“Kashe wannan budurwar da kona gawarta aiki daya ne kuma da yawa sannan bai kamata a bar shi ya sake faruwa da sunan addini ba. Kuma ina so na gargadi wasu shugabannin addinai, wadanda suka ce akwai bukatar a keta iyaka.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

“A kasa da ke da damokradiyya, idan aka keta maka iyaka, ka kaiwa hukumomin da suka dace kara sannan ka bar hukumomin doka su yi aikinsu, yayin da nake rokon dukkan kiristoci da su mutunta sauran addinai da ke kewaye da ku."

Da yake bayyana cewa babu wanda ke da ikon kawo karshen ran wani mutum, Ayokunle ya ce:

“Idan har muna ta magana ga gwamnatinmu kuma basu dauki wani mataki mai tsauri na hukunta wadanda suka aikata laifin ba, toh dole duniya gaba daya ta ji. Akwai bukatar mu daukaka lamarin zuwa al’umman kasa da kasa don su taimaki kiristocin Najeriya."

Malamin addinin ya kuma bayyana lamarin Deborah a matsayin mai tunzurarwa da rashin tausayi.

'Mun bar wa Allah' Iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto sun yi magana bayan binneta

A wani labarin, mun ji cewa mahaifin Debora Samuel, wacce aka kashe kan zargin ɓatanci a Sakkwato, Emmanuel Garba, ya bayyana cewa iyalansa sun ɗauki abun da da ya faru a matsayin kaddara daga Allah.

Kara karanta wannan

Igbo bai da amana, bamu yarda a ba su shugabancin kasa ba: Kungiyoyin Arewa CNG

A ranar Asabar aka birne gawar Debora a mahaifarta da ke Tungan Magajiya. ƙaramar hukumar Rijau a jihar Neja, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A wata zantawa da Dailypost, Garba, ya ce iyalansa sun shiga ƙunci bisa kisan Debora, amma ya ce ba abin da zasu iya yi game da lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel