Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

  • Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar gani da ido a wajen da tukunyar gas ta fashe a jihar Kano
  • Osinbajo wanda ke neman takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya kuma yi jaje ga mazauna da yan uwan wadanda lamarin ya shafa
  • Tun farko mataimakin shugaban kasar ya je Kano ne domin zantawa da wakilan APC a jihar kan kurinsa na son darewa kujerar Buhari

Kano - Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a jihar Kano.

An tattaro cewa an gano gawarwakin mutane tara, yayin da wasu da dama suka jikkata a yayin faruwar lamarin a safiyar ranar Talata.

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano
Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano Hoto: The Cable
Asali: UGC

Osinbajo wanda ya kasance a Kano domin ganawa da wakilan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan kudirinsa na son zama shugaban kasa, ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mun zo nan ne don mu fara ganema idanunmu abun da ya faru da kuma jajantawa mazauna yankin da iyalan da suka rasa nasu da masu yaran da suka jikkata.
“An fada mani cewa wannan bam ne kuma mutum tara sun mutu sakamakon faruwar lamarin.
“Wannan abun bakin ciki da takaici ne sosai.”

Hakazalika, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna, jami’an tsaro da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) sun kasance tare da Osinbajo a wajen.

Ga karin hotuna daga ziyarar:

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano
Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano Hoto: The Cable
Asali: UGC

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano
Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano Hoto: The Cable
Asali: UGC

Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Fashewar Tulun Gas, Ta Ce Ba a Makaranta Abin Ya Faru Ba

A wani labarin, gwamnatin Jihar Kano, a ranar Talata ta ce ba a makaranta ne fashewar tulun gas ya faru a Sabon Garin Kano ba, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Kwamishinan Labarai, Malam Muhammad Garba, wanda ya yi karin hasken ya ce fashewar ya faru ne a wani wurin ajiye abincin dabobbi 'da ke kallon makarantar' a Aba Road, Sabon Gari, karamar hukumar Fagge.

The Nation ta tattaro cewa wasu na fargabar cewa yan ta'adda sun fara kai hari makarantu a Kano bayan abin da ya faru a kusa da makarantar Winners Kid Academy.

Asali: Legit.ng

Online view pixel