Hoton dan siyasa rike da fostar Tinubu a masallacin Harami ya janyo cece-kuce

Hoton dan siyasa rike da fostar Tinubu a masallacin Harami ya janyo cece-kuce

  • Bayyanar hoton mai neman kujerar majalisar wakilai daga Legas dauke da fostar Tinubu a masallacin harami ya janyo cece-kuce
  • Da yawa daga cikin 'yan Najeriya sun yi mamaki tare da alakanta hakan da makauniyar soyayya da ake wa shugabanni
  • A tsokacin wasu kuwa, sun ce hakan rashin wayewa, ilimi da gogewa ne, ko kuma yana yin hakan ne saboda wata manufa tasa ta daban

A cikin makon nan ne hoton dan siyasa mai neman kujerar majalisar wakilai a jihar Legas ya bayyana dauke da fostar Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar APC a masallacin Harami ya bayyana.

Babu shakka jama' sun yi mamaki tare da al'ajabin faruwar wannan lamarin, duk da dai an san addu'a yake ta neman dacewa.

Hoton dan siyasa rike da fostar Tinubu a masallacin Harami ya janyo cece-kuce
Hoton dan siyasa rike da fostar Tinubu a masallacin Harami ya janyo cece-kuce. Hoto daga aminya.dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan wallafa hoton, Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin tsokacin da 'yan Najeriya suka dinga yi a kan wannan sabon salon.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Mujahid Ibrahim cewa yayi: "Sakarcinmu ashe har ya kai wannan matakin. Ina tunanin ko mutuwa 'yan Najeriya suka yi, za su kasance 'yan siyasa a kaburburansu. Rashin tunani da rashawa ta mayar da 'yan siyasarmu marasa kunya, a bayyane kana iya ganin yunwarsu da kwadayin hayewa madafun iko. Allah ya gyara, Allah yasa mu dace, Allah ya shirye mu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ibrahim Ibn Owuri cewa yayi: "Hukumomi a Saudi ya dace su dauka matakin gaggawa wurin fatattakar wadannan hadamammun 'yan siyasar daga garin nan mai tsarki."
Abdullahi Sa'ad Ibn Gayawa ya ce: "Ya dace a binciki kwakwalwar! Dan Najeriya ne kadai zai iya yin hakan. Daukar hoto rike da takardu ana kiran sunayen jama'a. Rike fostar 'yan takara. Iyayen don Allah ku ilimantar da 'ya'yanku addinin Musulunci ta yadda ba za su yi wadannan abubuwan ba."

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Aliyu Lawal Namadan yace: "Gaskiya wasu daga cikin mutanen kasar mu sun samu matsala. 'Yan Kanyywood sun kai Naziru, yanzu kuma dan siyasa ya je da fosta. Wata ta rubuta sunan saurayinta, wani ya kai karar matanshi kuma duk ana dauka ana nunawa duniya. An maida wurin bautar Allah wurin drama."
Usman S Narkuta cewa yayi: "Wannan bala'i har ina? Tsabar son mulki da son kudi shi ne zai kai Najeriya ga halin da babu mai iya ceto ta."

A zantawar da Legit.ng tayi da Injinya Aliyu Abdurrahman Aliyu, dan asalin jihar Kano kuma malami a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, ya ce wannan al'amarin a mahanga da dama ba daidai bane.

A cewarsa: "Wato shi al'amarin ibada da addu'a, abubuwa ne guda biyu da jama'a da yawa suka kasa fahimta. Ko jahilci ne, ko tsabaragen makauniyar soyayya ne da ake wa shugabanni, musamman mu 'yan Najeriya.
"Ba laifi bane ka je Ka'aba ko Saudiyya kayi addu'a, amma ka tafi da fostar dan takara kana daukan hoto kana fada, kana yayatawa, kuskure ne a mahanga ta wayewa, addini, kai har da birgewa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

"Koda yake, sabanin mu 'yan Najeriya, hakan ne zai sa a san kana yi. Ko kuma wasu ma tura su aka yi don su je su yi addu'a, don haka yin hakan da nunawa shi zai tabbatar da sun yi.
"Amma a mahanga ta ilimi, ta gogewa, ta wayewa, ta sanin daidai, duk akwai kuskure mai tarin yawa. Balle kuma a ce addini. Don haka wannan ya yi ne saboda wata manufa tasa wacce shi kadai ya sani."

Tinubu ga matasa: Da sannu za ku jagoranci kasar nan, amma sai bayan na ɗana

A wani labari na daban, Bola Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya sanar da matasan Najeriya cewa za su zama shugabannin kasar nan ne bayan ya kammala wa'adin mulkinsa.

Ana ta assasa bukatar matasa su mamaye manyan ofisoshin siyasa na kasar nan wanda ya sa ake ta amfani da likau na #NotTooYoungToRun.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace wasu da dama a kauyen Sokoto

A yayin jawabi a ranar Lahadi a ziyarar da ya kai wa Lamidi Adeyemi, Alaafin na Oyo a fadarsa, Tinubu ya bukaci matasa da su bai wa dattawa wuri, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng