Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace wasu da dama a kauyen Sokoto

Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace wasu da dama a kauyen Sokoto

  • Yan bindiga sun farmaki al'ummar kauyen Taka Lime a karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto
  • A yayin harin, tsagerun yan bindigar sun kashe mutane takwas sannan suka yi awon gaba da wasu da dama
  • Sun bukaci al'ummar garin su biya kudin fansar wadanda suka sace miliyan 10 da kuma wani miliyan 10 a matsayin haraji idan har suna son zaman lafiya

Sokoto - Wasu da ake zaton yan bindiga ne kan babura sun farmaki kauyen Taka Lime da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto inda suka kashe mutane takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Wani mazaunin kauyen Taka Lime, wanda aka kashe matarsa da diyarsa a harin, Sani Takakume, ya ce yan bindigar sun farmaki kauyen ne inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace wasu da dama a kauyen Sokoto
Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace wasu da dama a kauyen Sokoto Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Takakume ya ce:

“Mun fito kwanmu da kwarkwatanmu dauke da makamai daban-daban don tunkarar maharan kuma mun yi nasarar kashe uku daga cikinsu sannan mun kama daya.
“Da suka gane cewa mazauna kauyen sun kashe uku daga cikinsu, sai suka kashe takwas daga cikin mutanen da ke tsare a hannunsu a matsayin ramuwar gayya.”

Ya ce abun bakin ciki shine cewa daya daga cikin yan bindigar ya zauna a cikinsu a kauyen tare da iyayensa.

Sharadin zaman lafiya

Rahoton ya kara da cewa yan bindigar sun riga sun bukaci a biya naira miliyan 10 a matsayin kudin fansar wasu daga cikin mazauna kauyen da aka sace sannan a biya wani naira miliyan 10 haraji kan al’ummar garin gaba daya idan har suna son a samu zaman lafiya a kauyen.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Jama'ar gari sun kadu da ganin makwabcinsu a cikin yan bindigar da suka farmake su

A gefe guda, mun ji a baya cewa mazauna garin Takakume a karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto sun kadu a ranar Lahadi lokacin da suka gano cewa tsohon makwabcinsu ne shugaban yan bindigar da suka farmake su.

Yan bindiga dauke da makamai sun farmaki garin a safiyar ranar Lahadi, amma sai yan banga suka yi musayar wuta da su, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar shugaban yan ta’addan, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel