Tinubu ga matasa: Da sannu za ku jagoranci kasar nan, amma sai bayan na ɗana

Tinubu ga matasa: Da sannu za ku jagoranci kasar nan, amma sai bayan na ɗana

  • Jigon jam'iyya mai mulki, Ahmed Bola Tinubu, ya sanar da matasan Najeriya cewa sai bayan ya zama shugaban kasa za su iya zama
  • Tinubu ya ce matasa na son wuce dattawa su yi shugabanci, korar tsofaffin za su yi daga gari idan suka haye mulki?
  • An dade da ana assasa bukatar matasa su shugabanci kasar nan, amma Tinubu ya sanar da cewa ba fa yanzu ba, sai ya ɗana kujerar

Bola Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya sanar da matasan Najeriya cewa za su zama shugabannin kasar nan ne bayan ya kammala wa'adin mulkinsa.

Ana ta assasa bukatar matasa su mamaye manyan ofisoshin siyasa na kasar nan wanda ya sa ake ta amfani da likau na #NotTooYoungToRun.

Kara karanta wannan

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

A yayin jawabi a ranar Lahadi a ziyarar da ya kai wa Lamidi Adeyemi, Alaafin na Oyo a fadarsa, Tinubu ya bukaci matasa da su bai wa dattawa wuri, TheCable ta ruwaito.

Tinubu ga matasa: Da sannu za ku jagoranci kasar nan, amma sai na ɗana
Tinubu ga matasa: Da sannu za ku jagoranci kasar nan, amma sai na ɗana. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter
"Ba za ku bai wa dattawa damar wucewa ba kuma ba ku zama shugabannin kasar ba. Idan kuma kuka zama shugabannin, korar mu daga gari za ku yi?" Tinubu ya bukaci sani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Za ku tsufa kuma za ku zama shugabannin kasa. Amma zan zama shugaban kasa kafin ku zama."

A watan Janairu, Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya sanar da burinsa na fitowa takarar neman kujerar shugaban kasa a shekarar 2023.

TheCable ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Legas din yana ta yawo a fadin kasar nan domin tuntubar masu ruwa da tsaki kan burinsa.

Kara karanta wannan

Magabatan Yarabawa za su ba ka nasarar zama shugaban kasa, Alaafin ga Tinubu

A watan Janairu, Tinubu ya ziyaraci jihar Oyo kan mutuwar Jimoh Oyewumi, Soun na Ogbomoso; Saliu Adetunji, Olubadan na kasar Ibadan da Alao-Akala, tsohon gwamnan jihar Oyo.

Ya gana da Seyi Makinde, gwamnan jihar a Ibadan.

A ranar 20 ga watan Janairu, ya ziyarci garin Minna, babban birnin jihar Niger domin tuntubar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, tsohon shugaban kasar mulkin soji kuma ya samu addu'o'insa.

Magabatan Yarabawa za su ba ka nasarar zama shugaban kasa, Alaafin ga Tinubu

A wani labari na daban, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi a ranar Lahadi, ya ce ya na da tabbacin cewa magabatan Yarabawa za su bai wa jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban kasar Najeriya a 2023.

Daily Trust ta ruwaitoo cewa, Sanata Tinubu ya ziyarci basaraken mai daraja ta farko na kasar Yarabawa a fadarsa da ke Oyo a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa APC Ta Sha Kaye a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Abuja, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Dauda

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, su biyun sun shige ganawar sirri bayan da tsohon gwamnan jihar Legas din ya isa fadar babban basaraken.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng