Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1

Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1

  • Jami'an sojoji da yan sanda sun yi nasarar dakile farmakin da yan bindiga suka yi yunkurin kaiwa kauyen Akwando da ke karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna
  • A yayin da ake musayar wuta tsakanin maharan da jami'an tsaro, an yi nasarar kashe daya daga cikin yan bindigar sannan an kwato bindigar AK47 cike da harsasai
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da ci gaban inda ta ce sauran miyagun sun tsere da raunuka

Kaduna - Wata tawagar hadin gwiwa ta yan sanda da sojoji sun yi nasarar dakile wani hari da aka yi yunkurin kaiwa kan kauyen Akwando da ke karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna a ranar Litinin.

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya bayyana a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, cewa dakarun sun halaka daya daga cikin maharan sannan suka kwato bindigar AK47 guda daya, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Saraki, Tambuwal Da Wasu 'Yan Takara 2 a PDP Sun Amince Da Fitar Da Ɗan Takara Ta Hanyar Sasanci

Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1
Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mista Jalige ya yi bayanin cewa tawagar ta yi aiki ne bayan ta samu rahoto da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun farmaki kauyen Akwando.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa nan take sai aka tura tawagar zuwa kauyen sannan suka yi nasarar dakile harin yan bindigar.

Vanguard ta nakalto Jalige yana fadin cewa:

“A lokacin da miyagun suka hangi jami’an sai suka bude wuta sannan yayin da sojojin suka mayar da wuta, daya daga cikin yan bindigar ya mutu sannan aka gano bindigar AK47 cike da harsasai 17. Sauran yan ta’addan sun tsere da raunuka.”

Mista Jalige ya kara da cewar an ajiye gawar dan ta’addan da aka kashe a babban asibitin Kachia yayin da ake ci gaba da bincike domin kamo yan bindigar da suka tsere.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

Ya kuma bayyana cewa an dawo da zaman lafiya a kauyen Akwando sannan ya roki jama’a da su kai rahoton duk wani da suka gani da raunin harbi ga hukumomi, inda ya basu tabbacin samun kariya.

Yadda aka kashe Sadiya da diyarta mai shekaru 4 a Kebbi sannan aka yanke wasu sassa na jikinsu

A wani labarin, rundunar yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kisan wata mata da diyarta mai shekaru hudu a gidansu da ke Birnin Kebbi, babbar birnin jihar a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu.

Premium Times ta rahoto cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kashe Sadiya Idris mai shekaru 25 da diyarta Khadija a daren ranar Lahadi a gidanta da ke yankin Labana Rice Mills a titin Sani Abacha, Birnin Kebbi.

Yan sandan sun bayyana cewa ba a ga wasu sassa na jikin uwar da diyartata ba. An tsinci gawar tasu ne a safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta da yan bindiga a Katsina, rayuka sun salwanta

Asali: Legit.ng

Online view pixel